Ondo: Gwamna Akeredolu Ya Dawo Najeriya Bayan Tsawon Lokaci Yana Jinya

Ondo: Gwamna Akeredolu Ya Dawo Najeriya Bayan Tsawon Lokaci Yana Jinya

  • Gwamna Rotimi Akeredolu na juhar Ondo ya dawo gida Najeriya daga ƙasar Jamus inda ya shafe dogon lokacin yana jinyar rashin lafiya
  • Matar mai girma gwamna da shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Ondo sun tabbatar da labarin dawowar gwamnan
  • Akeredolu na jam'iyyar APC ya ɗauki hutu rashin lafiya kana ya miƙa mulki ga mataimakinsa sannan ya kama hanya ya bar ƙasar nan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ondo - Alamu masu ƙarfi sun nuna cewa gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya dawo gida Najeriya daga hutun jinya da neman lafiyan da ya tafi ƙasar Jamus.

Gwamna Akeredolu ya bar Najeriya zuwa ƙasar Jamus watanni da dama da suka gabata domin jinyar rashin lafiyar da yake fama da ita, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo.
Ondo: Gwamna Akeredolu Ya Dawo Najeriya Bayan Tsawon Lokaci Yana Jinya Hoto: punchng
Asali: UGC

Rahonanni sun nuna cewa bayan shafe watanni yana jinya, gwamnan ya dawo gida Najeriya yau Alhamis, 7 ga watan Satumba, 2023.

Kara karanta wannan

To Fa: Atiku Abubakar Ya Shiga Sabuwar Rigima Yayin da Yake Shirin Ɗaukaka Kara Zuwa Kotun Ƙoli

Matar mai girma gwamnan, Misis Betty Akeredolu, ita ce ta tabbatar da dawowar mai gidanta a wani saƙo da ta wallafa a manhajar X watau tsohuwar Tuwita.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Majalisar dokokin jihar Ondo ta tabbatar da dawowar gwamna

Haka nan kuma shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Ondo, Mista Wole Ogunmolasuyi, ya tabbatar da labarin dawowar mai girma gwamna Rotimi Akeredolu ga 'yan jarida.

Ɗan majalisar dokokin ya ƙara da bayanin cewa yanzu haka, gwamnan yana gidansa da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

A jawabinsa, Mista Ogunmolasuyi ya ce:

"Muna ƙara gode wa Allah mai girma gwamna ya dawo ƙasar mu Najeriya. Ya sauka a babban birnin tarayya Abuja kuma daga nan ya wuce kai tsaye zuwa Ibadan."

Wata majiya mai karfi ta gwamnati ta tabbatar wa Vanguard cewa gwamnan ya dawo kasar nan kuma zai gana da muƙarrabansa ranar Juma’a a lbadan.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Faɗi Kalamai Masu Jan Hankali Game da Rasuwar Sheikh Giro Argungu, Ya Miƙa Ta'aziyya

A cewar majiyar, “Eh, zan iya tabbatar muku da cewa mai gida ya sauka, kuma ‘yan majalisar zartarwarsa zasu gana da shi ranar Juma’a a gidansa da ke lbadan."

"Gwamnan zai rubutawa majalisar dokokin jihar wasiƙa kafin ya koma bakin aiki."

DSS Ta Kama Jami'an Gwamnati Da Ke Karkatar da Tallafin da Ake Raba Wa Talakawa

A wani labarin kuma Hukumar DSS ta kama ma'aikatan gwamnati bisa zargin wawure wasu kayan tallafin da FG ta samar domin raba wa yan Najeriya.

Wasu daga cikin waɗanda ake zargin sun shiga hannun DSS ne a fitacciyar ƙasuwar Lafiya, babban birnin jihar Nasarawa inda suke sayar da kayayyakin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel