Dan Sanda Ya Harbi Yaro Da Kakarsa Wajen Rabon Kayan Tallafi a Jihar Neja

Dan Sanda Ya Harbi Yaro Da Kakarsa Wajen Rabon Kayan Tallafi a Jihar Neja

  • Harbin bindiga ya samu wani yaro da kakarsa bia kuskure a wajen rabon kayan abinci a yankin Rijau ta jihar Neja
  • An samu barkewar rikici a cibiyar rabon kayan tallafin lamarin da ya sa wani jami'in dan sanda yin harbi a iska don tarwatsa jama'a
  • Shugaban rundunar yan sandan reshen Rijau ya tsare jami'in da ya yi harbi domin gudanar da bincike kan lamarin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Niger - Wani jami'in dan sanda da aka tura cibiyar rabon kayan tallafi da ke unguwar Sale Mai Agogo a karamar hukumar Rijau ta jihar Neja, ya harbi wani yaro dan shekara 12, Sani Danlami da kakarsa, Nna kan kayan tallafi a garin.

Kamar yadda jaridar The Guardian ta rahoto, jami'in tsaron na aiki ne da ofishin rundunar na sashin Rijau.

Kara karanta wannan

Wike Ya Yi Babban Albishir Ga Yan Najeriya Kan Gwamnatin Tinubu, Ya Ce Romon Dadi Na Nan Tafe

Jami'in dan sanda ya harbi wani yaro da kakarsa a Neja
Dan Sanda Ya Harbi Yaro Da Kakarsa Wajen Rabon Kayan Tallafi a Jihar Neja Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Yadda jami'in dan sanda ya harbi yaro da kakarsa wajen rabon kayan tallafi

Lamarin wanda ya afku a ranar Lahadi da ta gabata, ya biyo bayan wani rigima da ya kaure a wajen rabon kayan tallafin a garin Rijau.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An tattaro cewa jami'in dan sandan da aka tura don sa ido a bangaren ya yi harbi a iska don tarwatsa dandazon jama'a, amma abun takaici sai harbi ya sami Danlami da kakarsa a hannayensu na dama yayin da suke hanyar zuwa wajen rabon kayan.

Sun kasance yan gudun hijira a sansanin yan gudun hijira da ke kauyen Inana.

Da yake amsa tambayoyi daga manema labarai, shugaban kwamitin rabon kayan abincin a karamar hukumar Rijau, Dr. Tukur Bello, ya ce lamarin ya afku ne bisa hatsari.

Bello, wanda ya kuma kasance kwamishinan jihar a ma'aikatar lafiya, ya ce an kwashi wadanda abun ya ritsa da su zuwa wani asibiti da ke kusa don basu taimakon gaggawa kafin aka dauki yaron wanda ya ji mugun rauni zuwa asibitin kwararru na IBB da ke Minna.

Kara karanta wannan

“Idan Lasifika Ba Zai Yi Aiki Ba, Ta Yaya Abuja Za Ta Yi Aiki”: Wike Ya Yi Wa Jami’an FCTA Wankin Babban Bargo

Ya bayyana cewa wasu bata gari ne suka haddasa rikicin inda suka mamaye sashin tare da kwashe wasu kayayyakin, wanda ya kai ga har aka yi harbin.

Ya ce:
"Mun kwashe su zuwa daya daga cikin asibitocin don basu taimakon gaggawa, an kula da kakar wacce ta ji rauni kadan kuma har an sallame ta.
"Da jin labarin, Gwamna Mohammed Umar Bago, ya yi umurnin yin duk mai yiwuwa don ceto rayukansu da kuma tabbatar da ganin sun samu cikakken kulawar likitoci."

An tsare dan sandan da ya yi harbin

Bello ya tabbatar da cewar DPO na ofishin yan sandan Rijau ya garkame jami'in dan sandan domin gudanar da bincike, rahoton Vanguard.

Legit Hausa ta nemi sanin yadda aka gudanar da rabon tallafi a jihar Neja inda mutane da dama suka koka kan yadda aka tafiyar da abun.

Wata matar aure mai suna Zainab Aliyu ta ce sam bata ji dadin yadda aka yi abun ba, ba tsari kwata-kwata.

Kara karanta wannan

A Kokarin Gyara A Harkar Ilimi, Abba Kabir Ya Dauki Mummunan Mataki Kan Wasu Shugabannin Makarantu 2 A Kano

Zainab ta ce:

“Gaskiya ban ji dadi ba, sam ba haka nay i tsammani ba, an kawo kayan abinci dan kadan ga dandazon jama’a sun taru. Ko kwatan mutanen da suka hadu basu samu ba aka ce wai ya kare. Abun dai sai wanda ya gani.”

Malama Safiya kuwa cewa ta yi taliyar indomie kawai suka gani. Tana mai cewa:

“A layinmu fa indomie aka raba. Yara a basu guda daya sannan manya guda biyu. Fisabilillahi wani radadi wannan zai rage a cikin wannan yanayi da ake ciki. Haka dai aka kare da hargitsi domin dai ko indomie dayan ba kowane ya samu ba. Allah ya kyauta amma dai da sake wannan rabo da aka ce an yi a jihar Neja.”

Mutane 24 sun mutu a wani hatsarin jirgin ruwa a jihar Neja

A wani labari na daban, mun ji cewa wani iftila'i ya auku a jihar Neja da safiyar ranar Lahadi, 10 ga watan Satumba, bayan wani jirgin ruwa ya yi hatsari a yankin Mokwa na jihar.

Ba a san adadin yawan mutanen da ke cikin jirgin ruwan ba, sannan ba a san takamaiman abin da ya haddasa haɗarin ba har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Asali: Legit.ng

Online view pixel