Yadda Motar Tanka Ta Murkushe Wata Matashiyar Budurwa Har Lahira a Jihar Neja

Yadda Motar Tanka Ta Murkushe Wata Matashiyar Budurwa Har Lahira a Jihar Neja

  • Motar tanka ta yi ajalin wata matashiyar budurwa a garin Minna, babban birnin jihar Neja
  • Wani direba da ke tukin ganganci ya buge yarinyar mai shekaru 16 zuwa daya bangaren inda wata motar tankar ta bi ta kanta
  • Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce ta kama dukka direbobin da ke da alaka da hatsarin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Niger - Rundunar yan sandan jihar Neja ta tabbatar da mutuwar wata matashiyar budurwa mai shekaru 16, Priscilla Galadima, wacce motar tanka ta murkushe har lahira a garin Minna.

Daily Trust ta rahoto cewa kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya sanar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar Alhamis, 31 ga watan Agusta.

Motar tanka ta murkushe matashiya a Neja
Yadda Motar Tanka Ta Murkushe Wata Matashiyar Budurwa Har Lahira a Jihar Neja Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Yadda motar tanka ta buge matashiya a Neja

Kara karanta wannan

Halin kunci: Jama'a Sun Farmaki Rumbun Abinci A Wata Jiha, Sun Kwashe Kayan Abinci Na Miliyoyi

Ya ce marigayiyar ta kasance mazauniyar unguwar Barkin-Sale da ke Minna, kuma tana kokarin tsallaka titi ne lokacin da motar ta buge ta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

"Da misalin karfe 10:00 na safiyar ranar Laraba wata motar Mercedes Benz dauke da lambar SUL 140 AJ wanda wani Daniel Joshua, mai shekaru 35 mazaunin Morris Minna ke tukawa, ta tawo daga hanyar Mandela za ta shatale-talen Shiroro.
"Amma a hanya, yana ta tukin ganganci sannan ya goga wata motar Toyota Yaris mai lamba RJA 375 AA wacca wani Abubakar Yahaya na Okada Road yake tukawa.
"Motar Mercedes din ta ki tsayawa yayin da mai motar Toyotan ya dungi bin sa don tsayar da shi. A cikin haka ne Benz din ya buge wata da ke tafiya a kafa, Priscilla Galadima mai shekaru 16 ta Barkin-Sale, wacce ke kokarin tsallaka titin ta shatale-talen Shiroro.

Kara karanta wannan

Kungiyar NURTW Ta Bayyana Shirin Da Ake Don Kai Ma Ta Hari a Babbar Sakatariyarta Ta Kasa

Abiodun ya ce an buge matashiyar zuwa daya bangaren, inda ya kara da cewa:

"Abun takaici, wata motar tanka da ke zuwa mai lamba JMT 576 YR wacce wani Ibrahim Lawal na Jembutu Yola ke tukawa, ta bi ta kan marigayiyar."

An kama direbobin motocin da suka haddasa abun

Ya bayyana cewa an dauki marigayiyar zuwa Babban asibitin Minna, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarta, rahoton Pulse.

Abiodun ya kara da cewar an kama direbobin sannan aka kai su ofishin yan sanda na Tudun Wada don ci gaba da bincike, yayin da aka ajiye gawar marigayiyar a dakin ajiye gawa na babban asibitin Minna.

Legit.ng ta zanta da wata ma’aikaciyar mai da ke da masaniya kan abun da ya faru inda ta tabbatar da lamarin.

Ma’aikaciyar wacce ta nemi a sakaya sunanta ta ce:

“Eh da gaske ne. Muna cikin aiki sai muka ga yan sanda wai direban da ya kawo mana mai ya buge wata yarinta ta mutu. Sun tisa keyarsa bayan ya sauke mai, a ofishin yan sanda ya kwana yanzu dai magana na chan wajensu.”

Kara karanta wannan

Jan aiki: Sojojin Najeriya sun lalata wata matatun mai da ake aiki ba bisa ka'ida ba

Fasto ya cinnawa wata wuta a wajen addu'a

A wani labari na daban, mun ji cewa Fasto Taiwo Odebiyi na Cherubim and Seraphim Church, Maberu Parish wacce ke a Offin a yankin Sagamu na jihar Ogun, ya shiga hannun jami'an ƴan sanda bisa cinnawa wata budurwa wuta.

Faston dai ya cinnawa budurwar mai suna Sukura Owodunni, mai shekara 21 a duniya wuta ne lokacin da ya ke yi mata addu'a ta musamman.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel