Azumin Bana: Wata Coci Tayi Rabon Kayan Abinci Ga Musulmai a Kaduna

Azumin Bana: Wata Coci Tayi Rabon Kayan Abinci Ga Musulmai a Kaduna

  • Wata coci a jihar Kaduna ta gudanar da rabon kayan abinci ga musulmai marasa ƙarfi domin watan azumin Ramadan
  • Cocin ta rabawa sama da mutum 1000 marasa ƙarfi kayayyakin abincin ne domin su gudanar da azumin bana cikin walwala
  • Shugaban cocin ya bayyana cewa sun yi hakan ne domin ƙara ƙarfafa danƙon zaman lafiya dake tsakanin mabiya addinan biyu

Jihar Kaduna- Cocin Christ Evangelical and Life Intercessory Ministry, Sabon Tasha, a ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, a ranar Laraba tayi rabon kayan abinci ga musulmai masu ƙaramin ƙarfi kimanin 1000, saboda azumin bana.

Wasu daga cikin kayan abincin an raba su ne ga Almajirai da mabarata a ƙarƙashin ƙungiyar Association of Persons with Disabilities, babban masallacin titin Kano, cikin birnin Kaduna. Rahoton Punch

Kara karanta wannan

Matar Mark Zuckerberg, Attajiri Mai Kamfanin Facebook ta Haife Masa Ɗiya ta 3

Azumi
Azumin Bana: Wata Coci Tayi Rabon Kayan Abinci Ga Musulmai a Kaduna Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Kayayyakin sun hada da buhunan shinkafa, buhunan masara, buhunan gero da butotoci.

Babban mai kula da lamuran cocin, fasto Yohonna Buru, yayin da yake tattaunawa da ƴan jarida bayan an kammala rabon kayayyakin, yace cocin tana son taimakon musulmai marasa ƙarfi fiye da mutum 1000 a Arewacin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Faston ya bayyana cewa rabon kayayyakin an yi shine domin rage raɗaɗin sauya fasalin kuɗi, ƙarancin man fetur da kuma hauhawar farashin kayan masarufi akan marasa ƙarfi na cikin al'umma.

Buru ya ƙara da cewa, wannan shirin na su ya ta'allaƙa ne kan ƙara danƙon zaman lafiya tsakanin mabiya addinan biyu a jihar da kuma yankin gaba daya. Rahoton Vanguard

“Muna kuma rama biki ne kan karamcin da Hajiya Ramatu Tijjani, ta nuna na rabawa zarawa da marayun coci, buhunan shinkafi, kuɗi da sababbin kayan sanyawa a lokacin bukukuwan Kirismeti da Easter." Inji shi

Kara karanta wannan

25 Sun Mutu, 10 Sunji Munanan Raunuka a Wani Mummunan Hatsarin Mota a Bauchi

Ba a Ga Jinjirin Watan Ramadana Ba a Kasar Saudiyya, Alhamis Take Azumi

A wani labarin na daban kuma, ƙasar Saudiyya ta bayar da wata muhimmiyar sanarwa kan azumin watan Ramadan na wannan shekarar.

Hukumomi a ƙasar ta Saudiyya sun bayar da sanarwar cewa ba a ga jinjirin watan Ramadan ba a faɗin ƙasar a ranar Talata da aka duba.

Hakan na nufin watan azumin Ramadan a ƙasar zai fara ne a ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel