Bankin CBN Ya Kama Wani Dan Canji da Ke Siyar Da Dala Kasa Da Naira 700

Bankin CBN Ya Kama Wani Dan Canji da Ke Siyar Da Dala Kasa Da Naira 700

  • Babban Bankin Najeriya, CBN na farautar sauran ‘yan canji bayan samun wani da karya dokar siyar da Dala a kasuwa
  • Bankin CBN ya kama wani dan canji mai suna ‘Crown Agent’ kan zargin siyar da Dala kasa da yadda ake siyarwa a hukumance
  • Babban bankin na zargin dan canjin da siyar da Dala da araha kan kasa da Naira 700 wanda hakan ya sabawa dokokin bankin

FCT, Abuja – Babban Bankin Najeriya (CBN) ta fara binciken wani dan canji da ake kira ‘Crown Agent’ kan siyar da Dala kasa da yadda ya kamata a siyar.

Rahotanni sun tabbatar da cewa zuwa jiya Talata 5 ga watan Satumba ana siyar da Dala kan Naira 744 a kasuwanni, Legit.ng ta tattaro.

CBN ta kama dan canji mai siyar da Dala da araha
Bankin CBN Na Bincike Kan Masu Siyar Da Dala Da Araha. Hoto: CBN.
Asali: Getty Images

Meye CBN ke zargin dan canjin?

Kara karanta wannan

Karauniya Yayin Da Aka Sanar Da Sabon Farashin Gas Sabanin Yadda Tinubu Ya Yi Alkawari A Baya, Bayanai Sun Fito

CBN na zargin dan canjin da siyar da Dalar kasa da Naira 700 wanda ya yi araha da yawa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mukaddashin CBN, Folashodun Shonubi shi ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai inda ya ce su na kan binciken dan canjin.

Babban bankin ya sha alwashin zakulo dukkan masu irin wadannan halaye kamar yadda Punch ta tattaro.

Ya ce:

“A cikin ‘yan kwanakin nan muna farautar wadanda ke kawo kudade tare da siyar da su da araha ba bisa ka’ida ba, daya daga ciki shi ne ‘Crown Agent’.
‘Mu na da tabbacin akwai wadanda ba sa bin dokokin canjin kudade kamar yadda aka tsara a hukumance, za su ji daga gare mu nan ba da jimawa ba.”

Wannan na zuwa ne yayin da bankin ya himmatu wurin tsaftace harkar canji don tabbatar daidaito da kuma da bin doka da tsari.

Kara karanta wannan

Sanusi II Ya Yi Magana, Ya Haska ‘Barnar’ da Gwamnatin Buhari Tayi a Shekaru 8

Masu canji da CBN ta amince da su a wasu jihohi

Jerin ‘yan canji daga jihohi da su ka fi yawa da bankin CBN ya amince da su a kasar:

1. Legas – 2,958

2. Abuja – 1,179

3. Kano – 981

4. Anambra – 259

5. Kaduna – 55

6. Abia – 50

7. Oyo – 32

8. Enugu – 25

9. Rivers - 24

NNPC Ya Ciwo Bashin Dala Biliyan 3 Don Gyara Farashin Naira

A wani labarin, Kamfanin mai na NNPC ya ciwo bashin Dala biliyan uku don kawo daidaito a darajar Naira.

Kamfanin ya samu nasarar ciwo bashin ne a bankin AFRIEXIM da ke birnin Cairo a kasar Masar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel