Jihohi 10 da sukayi zarra wajen ilimin boko a Najeriya, Duba ko jihar ka ta sami shiga

Jihohi 10 da sukayi zarra wajen ilimin boko a Najeriya, Duba ko jihar ka ta sami shiga

Ilimi dai shine jigon cigaban duk wata kasa a duniya, shi kuma yake kawo bunkasar tattalin arziki da inganta rayuwar mutane kasar. Duk da haka, akwai wasu jihohi/kasashe da suka 'dara wasu wajen yawan masu ilimin. Sai dai kash... babu ta Arewa ko daya da ta shallake mizanin

Mu sani cewa neman ilimi ba abu bane mai sauki, yana bukatar kudi, lokaci, lafiya da kuma kwazo. Ku sani cewa ba wai yawan makarantu bane kawai ke nuna cewa al'umma nada ilimi, dole sai jama'a sun dage wajen zuwa makarantun domin su sami ilimin.

Jihohi 10 da sukayi zarra wajen ilimi a Najeriya
Jihohi 10 da sukayi zarra wajen ilimi a Najeriya

A shekarun baya, jihohin kudu maso yamma ne sukafi fice wajen neman ilimi a Najeriya, shin ko abin ya canza wannan shekaran?

Ko buyo mu domin mu zayyano muku jihohin da sukafi yawan masu ilimi a Najeriya.

Anyi la'akari da abubuwa daban-daban wajen tantance jihohin da sukafi yawan masu ilimi, kamar:

1. Adadin wanda suka iya rubutu da karatu

2. Yawan makarantun da ke jihar

3. Yawan masana da farfesoshi

4. Yawan mata da ke zuwa makaranta da dai sauransu.

Bayan la'akari da abubuwan da muka jera a sama, Hukumar da alhakin kididigar yawan jami'o'in Najeriya 'National University Commission Statistics' ta fitar da wannan jerin jihohin da Legit.ng ta kawo muku.

Jerin jihohin da sukayi zarra wajen ilimi a Najeriya

10. Jihar Ogun

Jihohi 10 da sukayi zarra wajen ilimi a Najeriya
Jihohi 10 da sukayi zarra wajen ilimi a Najeriya

Jihar na da makarantu kamar Odogbolu College, Sagamu College, Federal Government Girl's College, makarantun gaba da sakandari kuma sun hada da, Jami'ar koyon aikin noma na tarayya, Moshood Abiola Polytechnic, Olabisi Onabanjo University da sauransu.

09. Jihar Ondo

Jihohi 10 da sukayi zarra wajen ilimi a Najeriya
Jihohi 10 da sukayi zarra wajen ilimi a Najeriya

Jihar sun sha fadi tashi tun zamanin Baba Adekunle Ajasin har zuwa Dr. olusegun Mimiko. Kamar yadda Hope Newspaper ta bada rahoto, jihar a baya tana cikin jihohi biyar da sukafi yawan masu ilimin.

08. Jihar Bayelsa

Jihohi 10 da sukayi zarra wajen ilimi a Najeriya
Jihohi 10 da sukayi zarra wajen ilimi a Najeriya

Kamar yadda jaridar Vanguard ta bada rahoto, misalin kudi naira biliyan 40 ne gwamnatin jihar ta ware wa fanin ilimi, A cewar kwamishinan kudi na jihar, anyi amfani da kudin wajen gina-ginen ajujuwa da sauran dakunan karatu. Da alama kwaliyar ta fara biyan kudin sabulu.

07. Jihar Osun

Jihohi 10 da sukayi zarra wajen ilimi a Najeriya
Jihohi 10 da sukayi zarra wajen ilimi a Najeriya

Sabon tsarin gwamna Ogbeni Rauf Aregbesola na inganta ilimin primary yana cikin abubuwan da jihar ta sa a gaba. Bisa ga dukkan alamu, hakar ta fara cin ma ruwa.

06. Jihar Abia

Jihohi 10 da sukayi zarra wajen ilimi a Najeriya
Jihohi 10 da sukayi zarra wajen ilimi a Najeriya

Jihar na da jami'o'i guda 4 na kece raini, sune; Rhema University, Gregory University, Abia State University da kuma Michael Okpara University of Agriculture. Zaman lafiya da akeyi a jihar yana daga cikin abin da ke kara jawo hankalin masu saka jari a harkar ilimi.

05. Jihar Anambra

Jihohi 10 da sukayi zarra wajen ilimi a Najeriya
Jihohi 10 da sukayi zarra wajen ilimi a Najeriya

Jihar ta shahara wajen aikin karafe da kuma aikin gine-ginan tukwane, randuna da kuma gumaka. Jami'ar Nnamdi Azikiwe itace kan gaba wajen fasaha kere-keren karafa dama dai abin da jihar tafi maida hankali a kai kenan.

04. Jihar Enugu

Jihohi 10 da sukayi zarra wajen ilimi a Najeriya
Jihohi 10 da sukayi zarra wajen ilimi a Najeriya

Jihar dai inda aka gina jami'a na farko a Najeriya wato University of Nsukka, jihar tana da makarantu da dama wadanda sukafi maida hankali kan ilimin kimiya da fasaha. Ko wace unguwa a kala tana da makaranta guda daya na gwamnati.

03. Jihar Legas

Jihohi 10 da sukayi zarra wajen ilimi a Najeriya
Jihohi 10 da sukayi zarra wajen ilimi a Najeriya

Jihar Legas tana daga cikin jihohi masu arziki a Najeriya, harkar ilimi a jihar ma ba koma baya bane. Ba abin mamaki bane a samu jihar a wannan jerin jihohin masu yawan yan boko.

02. Jihar Delta

Jihohi 10 da sukayi zarra wajen ilimi a Najeriya
Jihohi 10 da sukayi zarra wajen ilimi a Najeriya

Jihar na daya daga cikin wanda sukayi fice wajen neman ilimi a Najeriya, mafi yawan makarantun jihar sunfi maida hankali ne wajen ilimin albarkatun man fetur.

01. Jihar Imo

Jihohi 10 da sukayi zarra wajen ilimi a Najeriya
Jihohi 10 da sukayi zarra wajen ilimi a Najeriya

Cibiyar ilimin jihar tana babban birnin jihar ne wato Owerri. Birnin yayi suna wajen yawan makarantu a duk fadin Najeriya.

DUBA WANNAN: Makarantar horas da soji da ke Kaduna ta fitar da sunayen daliban da sukayi nasarar shiga

A rahoton da jaridar Premium Times ta kawo, ya nuna cewa jihohin arewa sune ke jan jiki wajen ilimin na Boko, a arewacin Najeriya jihar Plateau na take kan gaba.

Idan dai Najeriya bata dage wajen neman ilimi ba, bazata iya gogaya da sauran kasashen duniya ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel