Shari'ar Zaben Shugaban Kasa: Sojoji Da 'Yan Sanda Sun Gargadi Masu Shirin Gudanar Da Zanga-zanga

Shari'ar Zaben Shugaban Kasa: Sojoji Da 'Yan Sanda Sun Gargadi Masu Shirin Gudanar Da Zanga-zanga

  • A ranar Laraba, 6 ga watan Satumba ne dai Atiku, Tinubu da Peter za su san makomarsu
  • Hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓe zai tabbatar da cewa Tinubu ne ya lashe zaben na watan Fabrairu ko akasin haka
  • Gabanin yanke hukuncin da ake dako, rundunonin soji da 'yan sanda sun gargaɗi mutane kan shirya duk wani nau'i na zanga-zanga

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Gabanin yanke hukuncin da ake jira kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta yi a ranar Laraba, 6 ga watan Satumba, jami'an tsaro sun fitar da wani gargadi.

Sun ce ba za su lamunci duk wani nau'i na tada hayaniya ba a babban birnin tarayya da ma sauran biranen da ke faɗin ƙasar nan in ji rahoton The Punch.

Jami'an tsaro sun gargaɗi masu shirin tayar da hankulan jama'a
Jami'an tsaron Najeriya sun aike da muhimmin gargadi ga masu shirin gudanar da zanga-zanga. Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Jami'an soji sun gargaɗi masu shirin gudanar da zanga-zanga

Kara karanta wannan

Nasara: 'Yan Sanda Sun Ceto Mutane 3 da Aka Sace a Zaria, Sun Tona Asirin Masu Hannu a Harin

Da yake jawabi gabanin yanke hukuncin, daraktan yaɗa labarai na hukumar tsaron Najeriya, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya shawarci masu shirin tada rikici da su canja tunani kamar yadda Business Day ta wallafa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya, an bayyana cewa mutane 'yan tsiraru ne za a bai wa damar shiga cikin kotun sauraron ƙararrakin zaɓen, a yayin da aka bukaci 'yan Najeriya su bibiyi shari'ar ta talabijin.

Tukur Gusau ya ba da tabbacin cewa ba za su zura idanu su bar wani ya yi abinda zai tayar da hankulan jama'a ba.

'Yan sanda sun gargadi masu shirin tada zaune tsaye

Rundunar 'yan sandan jihar Gombe ma ta fitar da saƙo na gargaɗi ga duk wasu masu shirin tayar da hayaniya a jihar gabanin yanke hukuncin.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar ta Gombe, Mahid Abubakar ne ya bayyana hakan, inda ya ce a shirye jami'ansu suke su daƙile duk wata barazana.

Kara karanta wannan

Hukumar DSS Ta Sako Dakataccen Karamar Hukumar Jihar APC da Ta Tsare, Bayanai Sun Fito

Ya shawarci duk wasu masu shirin tayar da rikici da su yi nesa da jihar ta Gombe, ko kuma su fuskanci matakin doka idan suka shigo hannu.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Oqua Etim, ya ba da umarnin a tsaurara tsaro a ko'ina domin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin al'umma.

DSS ta bankado wani shiri na tayar da hankulan al'umma

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan wani shiri da hukumar 'yan sanda na farin kaya (DSS) suka ce sun bankado, na yunkurin tayar da tarzoma da wasu 'yan siyasa ke ƙoƙarin yi.

Hukumar ta bayyana cewa an shirya zanga-zangar ne domin ɓata sunan gwamnatin Tinubu da jami'an tsaro ta bangaren abinda ya shafi tattalin arziƙin ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng