Kungiyar NLC Ta Shure Gana Wa da Gwamnatinn Tarayya Kan Yajin Aiki

Kungiyar NLC Ta Shure Gana Wa da Gwamnatinn Tarayya Kan Yajin Aiki

  • Jagororin ƙungiyar kwadago ta ƙasa NLC sun yi watsi da taron da gwamnatin tarayya ta shirya yau a Abuja
  • Shugabannin NLC ba su halarci ganawar ba wacce ma'aikatar kwadago da samar da ayyuka ta shirya domin rarrashinsu kada su shiga yajin aiki
  • Simon Lalong ya bukaci NLC ta TUC su ƙara hakuri kuma su bai wa FG ƙarin lokaci ta shawo kan mataalolinsu

FCT Abuja - Shugabannin ƙungiyar kwadago ta ƙasa (NLC) sun ƙaurace wa halartar taron da Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Simon Lalong, ya shirya a Abuja.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Ministan ya kira zaman ne da nufin shawo kansu su janye yajin aikin gargaɗi da suka shirya shiga a cikin makon nan.

NLC ta yi fatali da ganawa da FG.
Kungiyar NLC Ta Shure Gana Wa da Gwamnatinn Tarayya Kan Yajin Aiki Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Wakilin jaridar, wanda ke ɗauko rahoton abinda ke wakana a wurin taron, ya tattaro cewa shugabannin ƙungiyar 'yan kasuwa (TUC) ne ƙaɗai suka halarta karkashin shugaba, Festus Osifo.

Kara karanta wannan

Hukumar DSS Ta Sako Dakataccen Karamar Hukumar Jihar APC da Ta Tsare, Bayanai Sun Fito

Ganawar da aka shirya farawa da misalin ƙarfe 3:00 na yammacin yau Litinin, hakan ba ta samu ba sai ƙarfe 5:32 na yammaci sannan suka shiga taron, kamar yadda The Cable ta tattaro.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rahoto ya nuna cewa an hana kowa shiga taron, amma Ministan kwadagon ya roƙi 'yan jarida su yi musu uzuri yayin da su ke kokarin shawo kan batutuwa masu muhimmanci.

A ranar Juma’ar da ta gabata, NLC ta ayyana cewa ma’aikata a fadin kasar nan za su fara yajin aikin gargadi na kwanaki biyu daga ranar Talata 5 ga watan Satumba saboda halin kuncin da ‘yan Najeriya ke ciki.

FG ta roƙi yan kwadagu su yi hakuri

Yayin da yake hira da yan jarida ɗazu a Abuja, Ministan kwadago, Lalong ya ce bai samu zama da ƙungiyoyin kwadago ba kafin yau saboda har yanzu bai samu bayani daga ɓagarorin da abin ya shafa ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Tinubu Zata Gana da Ƙungiyoyin Kwadago Na Ƙasa Kan Muhimmin Abu 1

Ministan ya kuma yi kira da ƙungiyon NLC da TUC su dakatar da mambobinsu da sauran ƙawayensu daga shiga wannan yajin aikin.

Obasanjo: Gaskiyar Dalilin da Ya Sa Ya Dauko Yar'Adu Duk da Na San Ba Shi Da Lafiya

A wani rahoton kun ji cewa Olusegun Obasanjo ya bayyana gaskiyar yadda ya ɗauko Marigayi Yar'adua ya zama magajinsa duk da ya san ba shi da lafiya.

Tsohon shugaban kasa, Obasanjo ya ce zargin da ake jingina masa cewa ya san 'Yar'adua zai mutu shiyasa ya goya masa baya ba gaskiya bane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel