Jerin Wasu Kasashen Afrika da Ba a Taba Yin Juyin Mulki Ba Duk da Kitimurmurar Mulki

Jerin Wasu Kasashen Afrika da Ba a Taba Yin Juyin Mulki Ba Duk da Kitimurmurar Mulki

Bayanai da Powell da Thyne suka tattara sun nuna cewa daga cikin kasashe 54 na nahiyar Afirka, 45 sun fuskanci akalla yunkurin juyin mulki daya tun shekara ta 1950, inji rahoton Muryar Amurka.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Gabon dai ita ce ta karshe a jerin sunayen bayan da rundunar sojin kasar ta bayyana cewa ta hambarar da gwamnatin shugaba Ali Bongo ta hanyar juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar Laraba 30 ga watan Agusta.

Sai dai, akwai kasashen Afirka bakwai ba da su taba fuskantar juyin mulkin soja ba tun bayan samun 'yancin kai.

Kasashen da ba a taba juyin mulki ba
An bayyana inda ba a taba juyin mulki ba | Hoto: Cyril Ramaphosa/ Dr Lazarus Chakwera /Hage Gottfried Geingob
Asali: Facebook

Ga jerin kasashen kamar haka:

  1. Botswana
  2. Afirka ta Kudu
  3. Cape Verde
  4. Malawi
  5. Namibiya
  6. Eritrea
  7. Mauritius

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Akwai kuma wani jerin kasashe a Afirka, inda sojoji suka yi yunkurin juyin mulkin amma ba su yi nasara ba.

Kara karanta wannan

To fah: 'Yan Nijar sun ce sun gaji da alaka da Faransa, a fice musu daga kasa kawai

Jerin kasashen Afirka da suka fuskantar barazanar juyin mulkin da bai yiwu ba

Zambiya

An yi yunkurin juyin mulkin soji har sau uku a Zambia.

Maroko

Kasar Maroko ta fuskanci yunkurin juyin mulkin soji sau biyu da bai yi nasara ba a kasar da ke Arewacin Afirka.

Kenya

Kasar da ke gabashin Afirka ta fuskanci yunkurin juyin mulki sau daya wanda bai yi nasara ba a kasar a shekarar 1982 domin hambarar da gwamnatin shugaba Daniel Arap Moi.

Kamaru

Kasar Kamaru ta fuskanci yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a shekarar 1984 don hambarar da shugaba Paul Biya, in ji jaridar New York Times.

Mozambique

Yunkurin soji da bai yi nasara ba ya faru sau daya a Mozambique.

Senegal

Kasar Senegal ta fuskanci yunkurin juyin mulkin soja guda daya da bai yi nasara ba.

Angola

A cewar jaridar Washington Post, an yi yunkurin juyin mulki don hambarar da gwamnatin Agostinho Neto a shekarar 1977 a Angola.

Kara karanta wannan

Muje zuwa: Bayan rufe iyakan Gabon na kwanaki, shugaban soji ya fitar da sabuwar sanarwa

Djibouti

Ita ma Djibouti ta fuskanci yunkurin juyin mulkin soja daya da bai yi nasara ba.

'Yan Nijar sun nemi a kori Faransa a kasarsu

A wani labarin, dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a ranar Asabar a Yamai babban birnin jamhuriyar Nijar domin Faransa ta janye sojojinta kamar yadda rundunar sojin da ta kwace mulki a watan Yulin da ya gabata suka bukata.

Masu zanga-zangar dai sun taru ne a kusa da wani sansani na sojojin Faransa biyo bayan kiran da wasu kungiyoyin fararen hula da ke adawa da kasancewar sojojin Faransa a kasar suka yi.

Zanga-zangar ta tumbatsa ne bayan bullowar dandazon jama’a a wurin da lamarin ya faru a birnin Yamai da ke jamhriyar ta Nijar, Channels Tv ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel