Firgici Yayin Da Wata Akuya Ta Haifi Rabi Mutum Rabi Akuya a Jihar Kwara

Firgici Yayin Da Wata Akuya Ta Haifi Rabi Mutum Rabi Akuya a Jihar Kwara

  • Wani abin mamaki ya faru a wani ƙauye da ke jihar Kwara, inda akuya ta haifi ɗa mai siffar mutane
  • Lamarin ya faru ne a ƙauyen Adigun-Oke da ke ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara
  • Mutane da dama sun yi tururuwa zuwa ƙauyen domin ganewa idanunsu wannan abin al'ajabi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kwara - Wata akuya ta haifi ɗanɗa wanda wani ɓangare na jikinsa na mutum ne, yayin da wani ɓangaren kuma na akuya a ƙauyen Adigun-Oke, da ke ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara.

Wannan abin mamaki wanda ya ja hankulan jama'a ya faru ne a ranar Laraba ta makon da ya gabata kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta wallafa.

Akuya ta haifi rabi mutum rabi akuya a jihar Kwara
Akuya ta haifi ɗa mai kama da mutum a jihar Kwara. Hoto: Badamasi Usman
Asali: Facebook

Akuya ta haifi rabi mutum rabi akuya

Aishat Umar, wacce mijinta ne ke da akuyar, ta bayyana cewa 'ya'ya biyu ne ta haifa, inda ɗaya daga cikinsu ya zo da halittu irin na ɗan adam baya ga kunnuwansa da kafafunsa.

Kara karanta wannan

Hawaye, Yayin Da Ambaliyar Ruwa Ta Janyo Asarar Rayukan Mutane 3 a Garin Tsohon Gwamnan Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani daga cikin shugabannin al'umma na yankin mai suna Pa James Adeoye, ya bayyana cewa sun ga mutane suna ta tururuwa zuwan gidan da lamarin ya faru, inda suka je suka tarar da wannan abin mamaki.

Ya ce ɗaya daga cikin 'ya'yan da akuyar ta haifa jikinsa rufe yake da gashi irin na akuya, sai dai shi kuma ɗayan yana ɗauki da kamanni irin na mutane kamar yadda The Nation ta wallafa.

Mutane sun yi tururuwa don ganewa idanunsu

Wani shugaban al'umma a hirarsa da 'yan jarida ya bayyana cewa akuyar ta sha haihuwa a baya, amma ba ta taɓa yin irin wannan abun al'ajabi ba, kuma ba a taɓa ganin wani mutum ya tara da ita ba.

Wani mazaunin ƙauyen mai suna Lukman Onaade, ya bayyana cewa mutanen ƙauyen sun cika da mamaki saboda mutane da dama da ba su taɓa zuwa ƙauyen ba, sun zo domin ganin abin mamaki.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Hukumar DSS Ta Bankado Shirin Tayar Da Tarzoma a Kasa, Ta Magantu Kan Masu Hannu a Ciki

An bayyana cewa ɗan akuyar mai kama da mutane ya mutu bayan wani ɗan lokaci, inda mai akuyar ya binne shi a gidansa bayan dawowa daga gona.

Za ku iya kallon bidiyon ɗan akuyar da aka haifa da sassa na jikin mutum a jikinsa a bidiyon da aka ɗora a shafin Facebook na Kwarans Voice a ƙasa:

Bidiyon akuya da ta kori zaki ya ja hankulan jama'a

Legit.ng a baya ta yi wani rahoto kan bidiyon wata akuya da ta bi zaki ya ruga maimakon ya tsaya ya kasheta gami da yin kalaci da ita.

An bayyana cewa lamarin ya faru ne a cikin garin Benin babban birnin jihar Edo a wani gidan kula da dabbobin daji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel