Abin Mamaki Ya Faru Na Yadda Akuya Ta Sa Zaki Gudu, Bidiyon Ya Bar Jama’a Baki Bude

Abin Mamaki Ya Faru Na Yadda Akuya Ta Sa Zaki Gudu, Bidiyon Ya Bar Jama’a Baki Bude

  • Wani zaki ya guduwa akuya a maimakon ya kasheta ya cinye bayan da aka jefa masa dabbar a matsayin abincinsa
  • An yada faifan bidiyon wanda ya dauki yanayin da ba a saba gani ba a TikTok, kuma ya bazu tare da ba mutane da yawa mamaki
  • An ce an nadi bidiyon ne a gidan ajiye namun daji na Ogba da ke birnin Benin a jihar Edo, inda aka jefa akuyar ga zaki domin ya lamushe

Wata akuya ta farmaki wani zaki a gidan ajiye namun daji da ke Ogba a jihar Edo, inda aka ga sarkin dawan ya tserewa akuya, lamari mai ban mamaki.

A cikin wani faifan bidiyo da Reginal Bella ya saka a TikTok, an ga akuyar a cikin keji tare da zaki.

Mutanen da suke kallo sun yi tsammanin zakin zai buge akuyar ne tare da cinye ta cikin jin dadi nan da nan.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Tsere Daga Dazuzzuka, Sun Saki Wadanda Suka Sace a Arewa

Yadda zaki ya yi ta kansa yayin da akuya ta farmake shi
Zaki ya yi ta kansa bayan akuya ta farmake shi | Hoto: @reginalbella.
Asali: UGC

Sai dai, akasin haka ne ya faru domin akuyar ta samu karfin halin farmakar zakin cikin yanayi mai daukar hankali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zaki guduwa akuya a gidan ajiyar damun daji na Ogba

Zakin dai bai yi kokarin daukar mataki ba sai kawai ya yi kokarin tserewa ya koma gefe gudu a cikin kejin.

An yada bidiyon da rubutun:

"Wannan gidan ajiyar namun daji na Ogba ne, a cikin garin Benin, akuyar an kawo ta ne don zakin ya cinye, amma yanzu zaki ya tsorata da akuya."

Wadanda suka halarci gidan ajiye namun dajin sun yi ihu cike da mamakin ganin abin da ba a saba gani ba.

Kalli bidiyon a kasa:

Martani jama’a daga kafar TikTok

@samwise237:

"Wannan itace AKUWAR GASKIYA."

@nachee:

"Abin da zaki ke yi kenan. Ja da baya gareshi ba tsoro bane. Daga baya sai ya afkawa akuya."

Kara karanta wannan

“Budurwarsa Ta Ba Shi Kunya”: Malamin Addini Ya Yi Tsalle Daga Ginin Bene Mai Hawa 2, Ya Mutu a Anambra

@IREDIA:

"Bayan wasan kwaikwayon, meye ya faruwa da akuyar?"

@bigtriumphant:

"Jihar Edo ita ce zuciyar Najeriya komai na iya faruwa a can."

@PowerBoi3760536335722 ya ce:

“Haka Allah ke ba mu karfin fatattakar makiya.”

Labarin budurwa da zaki

A wani labarin, wata budurwa a kasar Indiya, ta tsallake rijiya da baya nayan da ta far ma zaki da sanda waidon ta ceci akuyarta da ya kawowa hari domin farauta.

Rupali Meshram, 'yar shekara 23 da haihuwa, ta ce bayan da ta ji akuyar ta na ihu, sai ta yi maza ta ruga ta nufi inda akuyar ta ke a wajen gidansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel