Manyan dalilai 3 da suka sanya ba’a cin naman akuya a jahar Sakkwato

Manyan dalilai 3 da suka sanya ba’a cin naman akuya a jahar Sakkwato

Wani bincike da jaridar Aminiya ta gudanar ya bayyana dalilin da yasa al’ummar Sakkwatawa basa cin naman akuya, duk da shahara da suka yi ta bangaren kiwon dabbobi.

Majiyar Legit.ng ta bayyana cewa a kasuwannin dabbobin jahar Sakkwato ana iya samun akuya maimatsakaicin girma a kan karamin kudi kamar N4,000, wanda hakan ke nuna rashin damuwa da akuya da jama’an yankin suke yi.

KU KARANTA: Gungun yan bindiga 2,000 sun mika makamansu ga gwamnan Zamfara

Sai dai binciken da majiyarmu ta gudanar game da wannan lamari ya bankado wasu dalilai da suka sa Sakkwatawa basa cin naman akuya kamar haka;

- Gudun yin dabi’a irin na Akuya:

Wani Farfesa a ilimin tarihi a jami’ar Usmanu Danfodi, Farfesa Mukhtar Umar Bunza ya bayyana cewa shi kansa a baya baya cin naman akuya, saboda gudun daukan halayya irin ta akuya.

- Danfodio baya cin naman Akuya:

Farfesan ya kara da wata hujjar da ta sa Sakkwatawa basa cin naman Akuya shi ne saboda an fada musu cewa Shehi Usmanu Danfodio wanda ya kafa daular Musulunci a Sakkwato baya cin naman akuya, don haka mutane irin Fulanin Torankawa ma basa ci.

Sai dai Farfesan yace amma a yanzu an samu raguwar tasirin wadannan hujjoji sakamakon karantarwar malaman Izala da suka tabbatar ma mutane babu inda Danfodio yace kada a ci naman Akuya.

- Tsoron daukan cutar kuturta:

Wani bahillace da majiyarmu ta tattauna da shi, Bello Abdullahi Tangaza ya danganta dalilin wasu mutane na kin cin naman akuya ga tsoron daukan cutar kuturta, ko kuma wasu cututtuka na daban kamar fitowar kuraje a jiki.

Sai dai wani mahaucin naman Akuya, Abubakar Mainama ya bayyana cewa mutane da dama sun saki wadannan al’ada na rashin cin naman akuya, inda yace a da sukan yankan akuya 100 a rana, amma a yanzu mutane basu da kudi a hannunsu saboda karayar arziki, bai fi su yanka 5 ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel