Shekaru 15 ga saurayi da jaraba ya kai lalata da akuya

Shekaru 15 ga saurayi da jaraba ya kai lalata da akuya

-An yankewa wani mutum hukuncin shekaru 15 a gidan kaso

- Wannan mutumi dai ya sadu da akuya ne mai ciki

- Mai shari'a Emeria Sunkutu tace ta tsorata da jin wannan batu

Shekaru 15 ga saurayi da jaraba ya kai lalata da akuya
Shekaru 15 ga saurayi da jaraba ya kai lalata da akuya
Asali: UGC

An yankewa wani mutum shekaru 15 a gidan Kaso a bisa tarawa da yayi da wata akuya mai ciki.

Wata kotu a kasar Zambia ta fara yankewa Reuben Nwamba shekaru 5 a gidan kaso yayin da wadanda sukai karar suka ga hukuncin bai musu ba suka daukaka karar zuwa kotun koli.

A halin yanzu wannan kuto ta Kasama ta yankewa mutumin dan shekaru 22 a duniya hukuncin shekaru 15 a gidan kaso tare da aiki mai tsanani.

DUBA WANNAN: Gara zaman talauci a gida da rayuwar wulakanci a bauta, balle fa nutsewa a yashi ko teku

Kotun tace Nwamba ya sabawa dokar kasar sannan duk wanda aka kara samu ya tara da wata dabbar to shima sai fuskanci irin wannan hukuncin.

Mai shari'a Emeria Sunkutu wadda ke shari'a a kotun Kasama tace tayi mamaki matuka da jin wannan batu.

Sannan daga karshe ta kara masa shekaru 10 akan wadancan 5 din ya koma shekaru 15.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng