Dangote Ya Karyata Jita-Jitar Cewa Su Na Siyar Da Siminti Da Araha Fiye Da Sauran Kasashen Afirka

Dangote Ya Karyata Jita-Jitar Cewa Su Na Siyar Da Siminti Da Araha Fiye Da Sauran Kasashen Afirka

  • Yayin da ake ta cece-kuce, kamfanin siminti na Dangote ya yi martani game da farashin siminti
  • Kamfanin ya karyata jita-jitar cewa farashin wasu kasashen Afirka ta Yamma ya fi na Najeriya araha
  • Daraktar gudanarwa na kamfanin, Arvind Pathak ya fadi amfani rarrabe farashin siminti na kamfanin da kuma sauran matsakaitan 'yan kasuwa

Kamfanin siminti na Dangote ya yi martani kan cece-kucen da ake yi kan siminti a Najeriya ya fi sauran kasashe Afirka ta Yamma tsada.

Kamfanin ya ce farashin siminti dai-dai ya ke wani lokaci ma yafi sauki a kasashen Afirka ta Yamma, Legit.ng ta tattaro.

Kamfanin Dangote ya yi martani kan jita-jitar karin farashin siminti a Najeriya
Kamfanin Dangote Ya Yi Martani Kan Jita-jitar Bambancin Farashin Siminti Da Sauran Kasashe. Hoto: Dangote Group.
Asali: Facebook

Meye kamfanin Dangote ya ce?

Kamfanin ya kara da cewa ba kamar yadda ake yadawa ba, babu batun karin farashin buhun siminti a kasar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Kwastomomi Sun Rage Zuwa Gida Karuwai a Kano, Gidan Magajiya Ya Dauki Zafi

Legit.ng ta tattaro cewa kamfanin siminti na Dangote shi ne yafi ko wane daraja a Najeriya a karshen watan Yuli.

Kamar yadda kamfanin ya sanar, farashin siminti a Okpella N4,010 yayin da ake siyar da shi a kan N4,640 a Ogbajana da Gboko da kuma Ibese.

Meye Dangote ya ce game da farashin?

Ya kara da cewa farashin na iya kaiwa N5,000 zuwa N5,300 idan aka yi lissafin kudin dakon kaya da sauran abubuwa.

Kamfanin ya ce ya fitar da wannan sanarwa ne don mai da martani kan korafin cewa farashin ya fi sauki a kasashe irinsu Benin da sauran makwabta a kan Najeriya.

Daraktan gudanarwa na kamfanin, Arvind Pathak ya bayyana muhimmancin bambance farashin kamfanin da kuma matsakaitan 'yan kasuwa.

Pathak ya ce:

"Muna kokarin samarwa miliyoyin kwastominmu kaya masu inganci a Nahiyar Afirka gaba daya.
'"A wannan kamfani na Dangote mun himmatu wurin tabbatar da ingantaccen kasuwanci ga masu ruwa da tsaki."

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Kwanaki kadan da yin ritaya, tsohon kakakin soja ya kwanta dama

Dangote Ya Tafka Asarar Naira Biliyan 480 A Sa'o'i 24

A wani labarin, Aliko Dangote, mamallakin kamfanonin Dangote a Najeriya ya yi asarar Dala miliyan 613 kwatankwacin Naira biliyan 483.87 cikin ko wane minti daya a sa’o’i 24.

Mujallar Forbes ta wallafa cewa Aliko Dangote yanzu ya dawo mataki na kasa da mallakar kudi Dala biliyan 10.5 a rahoton da ta fitar yau Laraba 9 ga watan Agusta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.