Kotu Ta Hana EFCC, ICPC Da CCB Kama Shugaban Yaki Da Cin Hanci Na Kano, Rimingado

Kotu Ta Hana EFCC, ICPC Da CCB Kama Shugaban Yaki Da Cin Hanci Na Kano, Rimingado

  • Babbar kotun da ke zamanta a jihar Kano ta haramta ci gaba da binciken Muhuyi Magaji, shugaban yaki da cin hanci na Kano
  • Hukumomin da ke yaki da cin hanci na EFCC da ICPC da kuma CCB na tuhumar shugaban yaki da cin hanci na Kano, Magaji Rimingado
  • Sai dai kotun ta haramtawa hukumomin ci gaba da binciken Rimingado har sai ta gama sauraran bahasi daga tushe

Jihar Kano - Babbar kotun jihar Kano ta haramtawa hukumomin yaki da cin hanci bincikar Muhuyi Rimingado kan zargin da ake masa.

Hukumomin da kotun ta haramtawa sun hada da EFCC da ICPC da kuma CCB wanda su ke kokarin kama shugaban yaki da cin hanci na jihar Kano.

Kotu ta haramtawa EFCC da ICPC kama Rimingado Kano
Kotu Ta Yi Hukunci Kan EFCC, ICPC Da CCB Na Kama Rimingado Na Kano. Hoto: Umar Ganduje, EFCC, Muhuyi Rimingado.
Asali: Facebook

Meye kotun ta ce wa EFCC kan Rimingado?

Kotun wanda Mai Shari'a Farouk Lawan Adamu ke jagoranta ya umarci hukumomin uku da su janye kudurinsu a wannan lokaci.

Kara karanta wannan

Halin kunci: Jama'a Sun Farmaki Rumbun Abinci A Wata Jiha, Sun Kwashe Kayan Abinci Na Miliyoyi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba a mantaba, Hukumar EFCC da kuma ta CCB na tuhumar ayyukan hukumar yaki da cin hanci ta jihar Kano karkashin jagorancin Rimingado.

Mai Shari'a Adamu ya ba da wannan umarni ne bayan sauraran Atoni Janar na jihar Kano, H. I Dederi wanda shi ne lauyan wanda ke kara, Daily Post ta tattaro.

Alkalin ya kuma umarci dukkan wadanda ke da alhakin a cikin shari'ar su dakatar da komai a yanzu.

Wane umarn ta bai wa EFCC kan Rimingado?

Umarnin kamar yadda Vanguard ta tattaro ta ce:

"Umarnin ta dakatar da dukkan masu kara ko wadanda ake kara daga daukar duk wani mataki daga yanzu har sai an saurari bahasi daga tushe.
"Umarnin ta kuma haramtawa wadanda ake kara da jami'ansu daga kamawa da gayyata da barazana ko musgunawa wani har sai an ji bahasi daga tushe."

Kara karanta wannan

PSC: Shugaba Tinubu Ya Sallami Manyan Jami'ai DIG 4, Ya Naɗa Waɗanda Zasu Maye Gurbinsu

Wadanda su ka shigar da kara sun hada da Atoni Janar na jihar Kano da Hukumar yaki da cin hanci da kuma shugabanta, Muhuyi Magaji Rimingado.

Yayin da wadanda ake kara su ne hukumomin yaki da cin hanci na EFCC da ICPC da kuma CCB.

EFCC Za Ta Bincki Rimingado Kan Badakalar Kudade

A wani labarin, Hukumar EFCC da kuma ta kula da da'a (CCB) na tuhumar shugaban yaki da cin hanci a Kano, Muhuyi Rimingado kan almundahana.

A cikin wata sanarwa, EFCC ta bukaci Rimingado ya turo daraktan kudi na hukumarsa don amsa tambayoyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel