Wasu ’Yan Bindiga Sun Kashe Sufeton Dan Sanda a Rivers, Sun Yi Awon Gaba da Bindiga da Hularsa

Wasu ’Yan Bindiga Sun Kashe Sufeton Dan Sanda a Rivers, Sun Yi Awon Gaba da Bindiga da Hularsa

  • Rahoton da muke samu ya bayyana yadda wasu tsageru suka hallaka jami’in dan sanda tare da sace bindigarsa da hularsa ta aiki
  • An bayyana yadda lamarin ya faru da kuma lokacin da aka yiwa dan sandan danyen aiki a yanayi mara dadi irin wannan
  • Ya zuwa yanzu, majiyoyi sun ce ana ci gaba da bincike don gano wadanda suka aikata wannan mummunan aikin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Rivers – Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe wani sufeton ‘yan sanda tare da sace bindigarsa, da kuma hular aikinsa a jihar Ribas.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan mummunan al’amari ya afku ne a daren Juma’a 25 ga watan Agusta a kusa da wani shahararren otal a Oroworukwo-Olu Obasanjo, a karamar hukumar Fatakwal.

Wata majiya ta ce tsagerun masu kisan gillar sun zo ne a kan wata mota kirar Toyota Corolla 2005 mai launin toka.

Kara karanta wannan

Shugaban 'Yan Bindiga Ya Ayyana Kansa a Matsayin Gwamnan Jihar Arewa? Gaskiya Ta Bayyana

An kashe dan sanda a Rivers
Yadda aka kashe dan sanda a Rivers | Hoto: Punch Newspaper
Asali: Facebook

An ce sun ga wanda suka kashen ne da fari, inda nan take suka farmake shi, suka yi awon gaba da bindigarsa AK-47, The Nation ta ruwaito.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Runduna ta tabbatar da faruwar lamarin

Jami’ar hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kuma ce wanda lamarin ya shafa, wanda ke aiki a jihar Bayelsa, ya raka wani babba ne zuwa jihar Ribas inda ‘yan bindiga suka farmake shi.

Iringe-Koko, wani jami’in ‘yan sanda, wanda ya bayyana jimami da faruwar lamarin, ya ce an fara gudanar da bincike don bankado abin da ke boye, Vanguard ta ruwaito.

Ana yawan samun labaran yadda ‘yan ta’adda suke hallaka jami’an ‘yan sandan Najeriya da ke yiwa kasa aiki, musamman a yankunan Kudancin Najeriya da ke fama da ‘yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, An Tsinci Gawar Shugabar Alkalai a Yanayi Mara Kyau a Jihar Arewa

Yadda aka kashe wani jami’in na daban

A wani labarin, wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe wani sufeton dan sanda mai suna Augustine Ukegbu a jihar Imo.

An kashe babban jami'in dan sandan ne a lokacin da ya je kauyensa da ke Umuoshike Ogbor a karamar hukumar Aboh Mbaise ta jihar Imo, jaridar Punch ta rahoto.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa wasu majiyoyi sun ce marigayin ya je gida ne tare da iyalinsa don bikin Easter.

Asali: Legit.ng

Online view pixel