Babbar magana: Yadda dan sanda ya kashe soja a Najeriya

Babbar magana: Yadda dan sanda ya kashe soja a Najeriya

Wani dan sanda da ba san ko waye ba a Najeriya da ke aikin gadin wani wurin hakar man fetur din kamfanin Shell an ruwaito cewa ya harbe wani soja har lahira a kauyen Odimodi dake a karamar hukumar Burutu ta jihar Delta dake a kudu maso kudancin kasar nan.

Majiyar mu dai ta ruwaito mana cewa lamarin ya faru ne a a ranar Asabar din da ta gabata biyo bayan wata 'yar gardama da ta rikide ta zama husuma a tsakanin su.

Babbar magana: Yadda dan sanda ya kashe sojo a Najeriya
Babbar magana: Yadda dan sanda ya kashe sojo a Najeriya

KU KARANTA: Matasa sun yi wa wani Gwamna Ihu a wajen taro

Sai dai kawo yanzu ba'a tabbatar da ainahin musabbabin rigimar ta su ba amma dai an hango su suna ta fada da cacar baki kafin daga bisani dan sandan ya narka masa harsashe wanda yayi sanadiyyar mutuwar sa.

A wani labarin kuma, Wani babba kuma sanannen malamin addini dake shugabantar rukunin majami'u na Eternal Light of World Christian mai suna Dakta Adol Awam ya fito ya bayyana kudurin sa na neman tikitin takarar gwamnan jihar Ebonyi a zaben 2019 mai zuwa a karkashin jam'iyyar APC.

Kamar yadda muka samu, Awam ya bayyana kudurin na sa ne a garin Abakalki, babban birnin jihar ta Ebonyi a jiya Litinin yayin da yake zantawa da manema labarai.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel