An kashe mutane 2, dan sanda guda ya bata bat a rikicin sansanin 'yan ci-rani na Allah-Onugwa

An kashe mutane 2, dan sanda guda ya bata bat a rikicin sansanin 'yan ci-rani na Allah-Onugwa

An tabbatar da mutuwar mutane biyu tare da bacewar wani dan sanda a wani rikici da ya barke a tsakanin mazauna Odekpe da Allah-Onugwa da ke yankin karamar hukumar Anambra ta Yamma a jihar Anambra.

An tura dan sandan da ya bata zuwa yankin domin tabbatar da zaman lafiya.

Rikicin ya barke ne a daren ranar Lahadi a wani sansanin 'yan ci-rani da ke yankin Igbamaka a shiyyar Ilushi.

Tun a cikin watan Yuli aka fara 'yan kananan rigingimu a tsakanin mazauna garuruwan biyu a kan wasu filaye da ke kan iyakokinsu.

Wani mazaunin Allah-Onugwa, David Uzor, ya ce suna zargin mutanen Odekpe da kai musu hari.

"Dumbin mutane daga Odekpe sun dira sansanin da jama'a ke zaman ci-rani. Sun fara harbin 'kan mai uwa da wabi' bayan isarsu, sun tarwatsa mutane.

"Sun kama dan uwan mahaifina mai suna Anthony Uzor, sun tafi da shi zuwa garin Odekpe inda suka yi masa kisan wulakanci. Da farko sun datse masa hannaye da kafafu, kafin daga bisani su yi masa yankan rago.

"Sun yi zargin cewa mutanenmu sun kashe wani mutumin garinsu, amma daga baya gaskiya ta fito, an gano cewa wani mutum ne daga jihar Edo ya kashe dan uwansu a kan wata matsala da ta shiga tsakaninsu," a cewarsa.

An kashe mutane 2, dan sanda guda ya bata bat a rikicin sansanin 'yan ci-rani na Allah-Onugwa
An kashe mutane 2, dan sanda guda ya bata bat a rikicin sansanin 'yan ci-rani na Allah-Onugwa
Asali: UGC

Uzor ya ce maharan sun harbe wani mutumin kauyen Igbamaka, sun raunata mutane hudu, sun lakadawa mata uku dukan tsiya, sannan sun dauke musu wayoyi.

DUBA WANNAN: Shehu Sani ya shawarci Buhari ya wakilta wasu dattijai hudu da za su warware matsalar rashin tsaro a arewa

Da ya ke mayar da martani a kan lamarin, wani basarake a kauyen Odekpe, Cif Austen Anerah, ya musanta zargin Uzor tare da bayyana cewa mutanen Allah-Onugwa ne suka fara kashe musu wani mutum mai suna Goddy Chukwuemeka.

A cewarsa, mutanen garin Allah-Onugwa suna kitsa karya domin jama'a da rundunar 'yan sanda su tausaya musu.

Da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sanda na jihar Anambra, Haruna Mohammed, a kan faruwar lamarin ya ce rikicin ya faru ne a wurin da kwamand din 'yan sandan Anambra basu da hurumi da shi.

Mohammed ya shawarci wadanda rikicin ya ritsa dasu su tuntubi ofishin rundunar 'yan sanda mafi kusa da wurin da rikicin ya faru.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng