Matsalar Tsaro: Yan Daba Sunyi Fito Na Fito Da Sojoji a Jihar Ebonyi

Matsalar Tsaro: Yan Daba Sunyi Fito Na Fito Da Sojoji a Jihar Ebonyi

  • Sojoji sun yi musayar wuta da wasu 'yan daba a ƙaramar hukumar Ohaukwu ta jihar Ebonyi
  • An bayyana cewa 'yan daban sun yi yinƙurin yin sata a cocin wani ƙauye da ke fama da rikici
  • Sai dai sojojin sun yi ƙoƙarin daƙile su, inda suka yi harbe-harbe har sai da suka fatattakesu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ebonyi - Wani rikici da ya sake ɓarkewa a Effium da ke karamar hukumar Ohaukwu ta jihar Ebonyi, ya rutsa da wasu sojoji da ke bakin aiki.

Jaridar The Punch ta tattaro cewa wasu 'yan daba ne da suka zo satar ƙarafa da sauran karikitan wata coci a yankin suka yi musayar wuta da wasu sojoji da ke bakin aiki.

Sojoji sun yi batakashi da 'yan daba a Ebonyi
Sojoji sun yi artabu da 'yan daba a jihar Ebonyi. Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Yadda 'yan daba suka yi fito na fito da sojoji

An bayyana cewa 'yan dabar sun zo ne ɗauke da manyan makamai, waɗandan suka yi amfani da su wajen korar mutanen da ake yankin da suka so yin ta'adi.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Rayuka Da Dama Sun Salwanta Bayan Wani Ginin Bene Ya Rufto a Kan Mutane

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan nan ne 'yan daban suka yi wa wata coci tsinke, inda suka yi harbe-harbe gami da ƙoƙarin satar ƙarafa da sauran wasu abubuwa masu muhimmanci a cikinta kamar yadda Vanguard ta wallafa.

Sai dai ƙarar harbe-harben na su ta sanya wasu daga cikin mazauna ƙauyen sanar da sojojin da ke bakin aiki, inda daga nan ne suka tunkari 'yan daban gadan-gadan.

Ganin sojojin ne ya sanya 'yan daban suka fara harbi, yayin da suma sojojin suka mayar da wuta har suka yi nasarar fatattakarsu.

Sojoji sun kama surukin Dogo Gide a Kaduna

A wani labarin na daban kuma, Legit.ng ta kawo muku rahoto kan nasarar da dakarun rundunar sojin Najeriya suka samu na kama surukin Dogo Gide.

Sojojin tare da hadin gwiwar 'yan sintiri, sun yi nasarar cafke surukin riƙaƙƙen ɗan ta'addan mai suna Kenkere a wata kasuwa da ke jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Wata Kungiya Ta Bukaci Ministocin Tinubu Su Yi Murabus, Ta Bayyana Dalilanta

Dogo Gide dai riƙakken ɗan ta'adda ne da ya addabi Arewacin Najeriya, inda ko a kwanakin baya sai da yaransa suka yi iƙirarin harbo wani jirgin sojin saman Najeriya.

'Yan bindiga sun harbe kwamandan rundunar tsaro a jihar Benuwai

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan kisan da wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka yi wa kwamandan rundunar kula da kiwon dabbobi na jihar Benuwai.

A shekarun da suka gabata ne dai jihar ya Benuwai ta kafa wata runduna ta musamman da za ta tabbatar da hana kiwon dabbobi a fili a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng

Online view pixel