Zan kawo karshen matsalar tsaro a jihar Zamfara - Mutawalle

Zan kawo karshen matsalar tsaro a jihar Zamfara - Mutawalle

Kamar yadda jaridar BBC Hausa ta ruwaito, gwamnan jihar Zamfara mai jiran gado, Muhammad Bello Mutawalle, ya haskaka hanyoyin da zai bi wajen yaye karfen kafa na matsalolin rashin tsaro da suka yiwa jihar dabaibayi.

Bayan da kotun koli da tabbatar da masa da nasarar lashe zaben jihar Zamfara, Mutawalle yayin wata hirar sa da manema labarai na BBC Hausa ya ce rashin adalci na daya daga cikin manyan dalilai da suka hana ruwa gudu wajen haifar da rashin tsaro a jihar Zamfara.

Zan kawo karshen matsalar tsaro a jihar Zamfara - Mutawalle
Zan kawo karshen matsalar tsaro a jihar Zamfara - Mutawalle
Asali: Twitter

Ko shakka babu Mutawalle wanda ya kasance tsohon shugaban kwamitin tsaro na majalisar wakilai ta tarayyar Najeriya, ya ce zai ribaci kwarewar sa wajen dasa hanyoyin warware kalubale na rashin tsaro da jihar Zamfara ke fuskanta a halin yanzu.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar Asabar da ta gabata ne hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, ta tabbatar tare da bayyana Bello Mutawalle, dan takara na jam'iyyar adawa ta PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Zamfara.

KARANTA KUMA: Akwai yiwuwar 'yan Najeriya 24m za su kamu da cutar tabin hankali - WHO

Hukumar INEC ta tabbatar da nasarar sa biyo bayan hukuncin da kotun koli ta yanke a ranar Juma'ar da ta gabata inda ta yi fatali da kuri'un da aka kadawa dukkanin 'yan takara na jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara a kowane mataki.

Sabon gwamnan mai jiran gado ya ce zai tabbatar da kyakkyawar mu'amala a tsakanin sa da gwamnatin tarayya ta APC wajen kulla hadin kai domin kawo zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'umma a jihar Zamfara.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng