Sababbin Ministocin Tinubu da Aikin da Shugaban Kasa ya ba Kowane Daga Cikinsu

Sababbin Ministocin Tinubu da Aikin da Shugaban Kasa ya ba Kowane Daga Cikinsu

  • Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da mutane 45 da za su rike masa ma’aikatun tarayya a kasar nan
  • Mai girma shugaban kasan ya ba kowa aikin da zai yi, an sanar da su ma’aikatun da za su rike tun tuni
  • Kafin yanzu, a kan bari sai ranar rantsuwa kafin minista ya fahimci aikin da ke gaban shi a Najeriya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Fadar shugaban kasa ta bi ta jero ministocin tare da zayyao nauyin da ya rataya a kan su. An fitar da wannan bayani ne a dandalin X da safen nan.

Aikin da aka ba Ministocin Najeriya

Shugaban kasa
Shugaban kasa Bola Tinubu ya rantsar da Ministoci Hoto: @nosasemota
Asali: Twitter

1. Muhammad Ali Pate

Shi zai kawo tsare-tsaren harkar kiwon lafiya da walwalar al’umma kuma ya kula da kiwon lafiyar jama’a, yaki da cututtuka da tabbatar da koshin lafiya.

Kara karanta wannan

Komai Ya Lafa, Majalisa Ta Fadi Inda Aka Samo Miliyoyin ‘Hutun’ da Aka Biya Sanatoci

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

2. Festus Keyamo

Tsare-tsaren da su ka shafi harkar jirgi a kasar nan su na hannun shi tun daga kula da filayen tashi, bincike a fannin jirage, kawo ka’idojin aiki da sauransu.

3. Uche Nnaji

Kawo cigaban fasaha da kimiyya, bunkasa masana’antu, kawo sauye-sauye na zamani da kuma zama sila tsakanin malaman makaranta da kirkire a zahiri.

4. Hannatu Musawa

Yayin da za ta kula tare da bada kariya ga al’adun da aka san Najeriya da su, lauyar za ta maida hankali wajen bankado hanyar samun kudin shiga a Najeriya.

5. Betta Edu

A matsayin minista, Betta Edu za ta taka rawar gani wajen tallafawa marasa karfi, yaki da talauci, taimakawa da jin kai da bada agaji idan an samu annoba.

6. Lola Ade John

Jawo mutane domin zuwa yawon bude ido a kasar nan, tabbatar da masu ziyara sun ji dadin zuwansu, fito da tarihin Najeriya, da tallafawa kananan masana’antu.

Kara karanta wannan

Sababbin Ma'aikatu Da Canje-Canje 14 Da Bola Tinubu Ya Kawo a Nadin Ministocinsa

7. Dele Alake

Shi zai kula da abin da ya shafi ma’adanan da ake da su irinsu zinari, makamashin kwal da ire-irensu.

8. John Enoh

Ayyukansa sun hada da kula da matasa, samar masu da ayyukan yi da goyon bayansu a wasanni.

9. Mariya Mahmud

Za ta taimaka wajen raya birane da karkaran da ke Abuja, rabon filaye da sauran abubuwan rayuwa.

10. Ibrahim Geidam

Tun daga tsara manufofi, duk abin da yake da alaka da yadda ‘yan sanda za su yi aiki da kyau.

11. Lateef Fagbemi

Shi zai kula da duk wani bangaren shari’a, bayan nan zai tabbatar da gwamnati ba ta sabawa doka.

12. Ekperipe Ekpo

Mai taimakawa Babban Ministan fetur, ayyukanta sun shafi sha’anin gas – hakowa da amfani da shi.

13. Ishak Salako

Kula da muhalli da lura da albarkatun kasa tare da yakar sauyin yanayi da gurbata wurin zama.

14. Uba M. Ahmadu

Shi kuma zai taimaka wajen tsare-tsare, hakowa da cin moriyar abin daya shafi karafa a kasar nan.

Kara karanta wannan

DSS: ‘Yan Ta’adda Sun Yi Shirin Kai wa Mutane Mugun Hari a Jirgin Abuja-Kaduna

15. Bello M. Goronyo

Aikinsa shi ne ya taimaka a samar da tsabtataccen ruwan sha da amfani mai tare da la’akari da tsabta.

16. David Umahi

Kawo abubuwan more rayuwa irinsu tituna, gadoji da sauransu, shi zai kula da gine-gine da gyaransu.

An rantsar da Ministoci a Aso Rock

A baya kun ji labari Lateef Fagbemi ya zama babban lauyan gwamnatin tarayyar Najeriya, ya gaji Abubakar Malami da ya bar ofis a Mayu.

Baya ga babban lauyan, an ratsar da Farfesa Joseph Utsev da Sanata Heineken Lokpobiri tare da sauran ministoci a fadar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel