Yan Sandan Birtaniya Na Tuhumar Tsohuwar Ministan Man Fetur Alison-Madueke Da Cin Hanci

Yan Sandan Birtaniya Na Tuhumar Tsohuwar Ministan Man Fetur Alison-Madueke Da Cin Hanci

  • 'Yan sandan Burtaniya sun gurfanar da tsohuwar ministar man fetur, Diezani Alison-Madueke a gaban kotu kan cin hanci
  • 'Yan sandan sun bayyana haka a ranar Talata 22 ga watan Agusta yayin da su ke zarginta da karbar na goro
  • Madueke ta kasance tsohuwar shugabar Kasashe Masu Arzikin Mai (OPEC) a lokacin mulkin Goodluck Jonathan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Landan - Wani sabon rahoto ya tabbatar da cewa 'yan sanda a Burtaniya sun gurfanar da tsohuwar ministar man fetur, Diezani Alison-Madueke a gaban kotu kan cin hanci.

Wannan na zuwa ne bayan yin bincike da Hukumar Laifuka ta Kasa (NCA) ta yi kamar yadda Reuters ta tattaro.

'Yan sandan Burtaniya sun kama Diezani Alison-Madueke
Yan Sandan Birtaniya Sun Kama Tsohuwar Ministan Man Fetur Alison-Madueke. Hoto: @Letter_to_Jack, Reuters.
Asali: Twitter

NCA ta ce Diezani ta karbi cin hanci a lokacin da ta ke rike da mukamin ministar man fetur don karbar kwantiragi na miliyoyin Daloli, Legit.ng ta tattaro.

Kara karanta wannan

Imaan Suleiman: Abubuwa 10 Muhimmai Game Da Mace Ta Farko A Matsayin Ministan Harkokin 'Yan Sanda

Meye ake zargin Diezani a kai?

Shugaban hukumar NCA, Andy Kelly ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Mu na zargin Diezani Alison-Madueke da karbar na goro don ba da kwantiragin miliyoyin Daloli a lokacin da ta ke rike da mukamin ministar man fetur a Najeriya."

Ana zargin ta samu kusan Yuro dubu 100 da wasu motoci da kuma jiragen hawa don shakatawa da iyalanta da kuma amfani da wasu kadarori na birnin Landan.

A ina Diezani ta ke?

Madueke wacce ke zaune a St. John's Wood da ke Landan za ta gurfana a gaban kotun majistare a birnin a ranar Litinin 2 ga watan Oktoba na sheakrar 2023.

Madueke mai shekaru 63 ta kasance cikin masu ruwa da tsaki a gwamnatin tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan.

Ta rike ministan arzikin man fetur daga shekarar 2010 zuwa 2015, ta kuma rike mukamin shugabar Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Mai (OPEC).

Kara karanta wannan

Meye zai faru? Shugaban matasan PDP ya bayyana kwarin gwiwar tsige Tinubu a mulki

Kotu Ta Umarci Kwace Kadarorin Diezani A Abuja

A wani labarin, Babbar kotun Tarayya da ke birnin Abuja ta ba da umarnin kwace dukkan kadarorin tsohuwar ministar man fetur, Diezani Alison-Madueke.

Mai Shari'a Mobolaji Olajuwon ta ba da wannan umarnin ne a ranar 24 ga watan Oktoba na 2022 a Abuja.

Cikin kadarorin da za a kwace akwai fuloti mai lamba 1854 da ke kan titin Muhammad Mudashir da kuma mai lamba 6 da titin Aso da ke yankin Maitama da Asokoro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel