Kotu Ta Ba da Umarnin Kwace Sauran Kadarorin Diezani Dake Abuja

Kotu Ta Ba da Umarnin Kwace Sauran Kadarorin Diezani Dake Abuja

  • Gwamnatin tarayya ta samu nasarar samun umarni daga kotu wajen kwace wasu kadarorin tsohuwar minista
  • Ana zargin tsohuwar minista a zamain shugaba Jonathan, Diezani da laifin sace kudade mallakin Najeriya
  • Hukumar EFCC na ci gaba da maka barayin gwamnati a kotu tare da tatso kudaden da ake zargin sun sata

FCT, Abuja - Babban kotun tarayya dake zama a Abuja karkashin mai shari'a Mobolaji Olajuwon ta umarci a kwacewar karshe na sauran kadarorin tsohuwar ministar arzikin man fetur, Mrs Diezani Alison-Madueke.

Wannan umarni na kotu na zuwa ne a ranar Litinin 24 ga watan Oktoban bana, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kadarori biyu da za a kwace a Abuja na Diezani sun hada fuloti mai laba 1854 a kan titin Muhammad Mahashir da kuma mai lamba 6 a titin Aso dake yankin Asokoro da Maitama a birnin.

Kara karanta wannan

Bako cinye gida: Kadan daga tarihin sabon Firayinministan Burtaniya Rishi Sunak

Diezani ta rasa wasu kadarorinta a babban binrin tarayya ABbuja
Kotu Ta Ba da Umarnin Kwace Sauran Kadarorin Diezani Dake Abuja | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

An kuma yi kiyasin cewa, akalla darajar wadannan kadarorin gidaje da za a kwace sun kai $2,674,418 N380,000,000 bi da bi, rahoton Daily Sun.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakazalika, za a kwace motocinta BMW mai lambar inji B8CV54V66629 da lambar rajista RBC155 DH da kuma kirar Jaguar mai lambar inji SAJAA.20 GRDMv43376 da darajarsu ta kai N36,000,000.

Kotun ta yanke hukuncin ne daidai da bukatar hukumar yaki da cin hanci da rashawa na neman ba ta damar kwacewar karshe na kadarorin da ake kyautata zaton Diezani ta siya da kudin da ta yi kwana dasu.

Yadda aka kwace wasu kadarorin Diezani a baya

A shekarar da ta gabata hukumar EFCC ta samu umarni daga kotu na kwace wasu kadarorin Diezani bisa zargin ta siye su da kudin haram.

Akwai kuma lokacin da hukumar EFCC ta buga a jarida cewa, tana tallata yin gwanjon kayan Diezani da ta kwata a ciki da wajen kasar nan.

Kara karanta wannan

Tashin hankanli: An gano sansanin horar da 'yan ta'addan IPOB, an kama kasurgumin kwamandansu

Bayan rasa mai saye, kotu ta mallakawa gwamnatin tarayya wadannan kadarori da aka kwato daga tsohuwar ministar.

Sarakunan Igbo Sun Afkawa Kotu, Sun Bukaci a Sako Nnamdi Kanu

A wani labarin na daban, sarakunan gargajiya shida na kabilar Igbo ne suka dumfaro kotun daukaka kara dake zama a babban birnin tarayya Abuja domin rokon a saki shugaban kungiyar ta'addanci ta IPOB, Nnamdi Kanu.

Sarakunan, dukkansu a cikin sutura ta gargajiya sun ce sun zo ne domin nuna goyon baya ga dansu, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Sun zauna a cikin kotun, sun kuma ji duk yadda aka yi kan bukatar gwamnatin tarayya na ci gaba da tsare Kanu a kalubalantar umarnin kotu na sakinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel