Kun ji fah: Ban saci ko kobo na talakawan Najeriya ba - Diezani Alison Madueke

Kun ji fah: Ban saci ko kobo na talakawan Najeriya ba - Diezani Alison Madueke

- Tsohuwar ministar man fetur Diezani Alison Madueke ta karyata zargin da ake yi mata na cewa ta saci kudin Najeriya

- Ta ce ko sisin kobo bata sata a kasar nan ba, kuma idan akwai mutumin da yake da hujja ya fito ya bayyana

- Ta kuma nuna rashin jin dadinta da irin zagin da 'yan Najeriya suke yi mata

Diezani Alison Madueke ta karyata zargin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da hukumar EFCC sukayi mata na cewar ta yi sama da fadi da dukiyar talakawar Najeriya a lokacin da take aiki.

Tsohuwar ministar man fetur din ta yi wata hira da fitaccen dan jaridar nan, Dele Momodu, inda ta karyata zargin da ake yi mata na sace dukiyar talakawa.

Mrs Diezani ta karyata zargin cewa ta yi almubazzaranci da dukiyar man fetur kamar Chris Aire, Kola Aluko, Tonye Cole, Igho Sanomi, da kuma wasu manyan masu kudi wanda ta hada alaka da su. Ta bayyana cewa ita matar aure ce kuma bata da wannan dabi'a ta bera.

KU KARANTA: Abinda maza ke so a jikin mace mai kyau irina shine su auremu su gama jin dadinmu su sake mu - Inji Fati KK bayan dawowarta fim

Tsohuwar ministar ta kuma karyata zargin sama da fadi da dala biliyan 20 da tayi na kudin man fetur. Ta kuma nemi duk wani wanda yake da hujja akan ta saci kudi su fito su bayyanawa duniya.

Ta kuma nuna rashin jin dadinta na akan 'yan Najeriya da suke zaginta, duk da irin kokarin da tayi na azurta da yawa daga cikinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel