Imaan Suleiman: Abubuwa 10 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Mace Ta Farko Da Ta Zama Ministar Harkokin 'Yan Sanda

Imaan Suleiman: Abubuwa 10 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Mace Ta Farko Da Ta Zama Ministar Harkokin 'Yan Sanda

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da mukaman ministoci a ranar Laraba 16 ga watan Agusta

Daga cikin wadanda aka nadan akwai tsoffin gwamnonin jihohin Rivers da Ebonyi da Jigawa da sauransu.

Imaan Sulaiman Ibrahim ita ce mace ta farko a matsayin karamar ministar Harkokin 'Yan Sanda, Legit.ng ta tattaro.

Abubuwa 10 muhimmai da ya kamata ku sani game da Imaan Sulaiman, Ministar harkokin 'Yan Sanda
Imaan Suleiman Ita Ce Mace Ta Farko Da Ta Zama Ministan Harkokin 'Yan Sanda. Hoto: Punch.
Asali: Facebook

Matashiyar da aka haife ta a jihar Plateau a baya ta rike babbar daraktar Hukumar Yaki da Safarar Mutane (NAPTIP).

Legit.ng Hausa ta kawo muku abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da sabuwar ministar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

1. Mahaifa

An haifi Imaan Sulaiman Ibrahim a jihar Plateau inda ta shafe rayuwarta a birnin Abuja.

Ta samu shaidar kammala firamare a makarantar firamare ta Jabi da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Kotun Ɗaukaka Kara Ta Tsige Shugaban Fitacciyar Jam'iyya Na Ƙasa, Ta Bayyana Sunan Sabon Shugaba

2. Digiri na biyu

Imaan ta kammala karatun digiri a fannin ilimin zamantakewa ta na da shekaru 19 yayin da ta yi digiri na biyu har guda biyu ta na shekaru 21.

3. Bautar Kasa

Imaan ta yi bautar kasa a kamfanin NNPC a ofishinsu da ke jihar Kaduna, Punch ta tattaro.

4. Digirin digirgir

A yanzu Imaan na kokarin kammala digirin digirgir a fannin tsaro a Jami'ar Tsaron Najeriya (NDA).

6. Aiki

Imaan ta fara aiki ne a Hukumar Tsara Bayanan Yanki (GIS) da ke Abuja.

7. Wayar da kan mata

Ta na daga cikin wadanda su ka kirkiri Cibiyar Beehive wanda yanzu ake kira cibiyar BumbleeBee Civic da ke kokarin wayar da kan mata masu sha'awar shiga siyasa.

8. 'Yar kasuwa

Ita ce babbar daraktar ciniki ta kamfanin kayan kwalliya da gyara jiki, Mary Kay.

9. Kwamishinar Tarayya

A watan Yuni na 2021, ta zama Kwamishinar Tarayya a bangaren kula da 'yan gudun hijira.

Kara karanta wannan

Sanatan Kano Ya Fadi Laifin da Tinubu Zai Yi a Yunkurin Aukawa Kasar Nijar da Yaki

10. Mukamai

Ta kasance mai ba da shawara a kan sadarwa na tsohon karamin ministan ilimi, Chukuemeka Nwajiuba.

An kuma nada ta mamba a kwamitin tattalin arziki na Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa a watan Satumba 2019.

10. Iyalai

Imaan Sulaiman ta yi aure kuma ta na da 'ya'ya guda uku.

Buhari Ya Nada Imaan A Matsayin Daraktar NAPTIP

A wani labarin, shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nada Imaan Sulaiman Ibrahim a matsayin babbar daraktar Hukumar Yaki da Safarar Mutane (NAPTIP).

Buhari ya bayyana haka ne ta bakin kakakinsa, Malam Garba Shehu a cikin wata sanarwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel