Coronavirus: Hukumar gwamnatin tarayya ta zaftare kashi 50 na albashin ma’aikatanta

Coronavirus: Hukumar gwamnatin tarayya ta zaftare kashi 50 na albashin ma’aikatanta

Sakamakon nakasu game da kudaden shiga da hukumar kula da tashoshin jiragen sama ta Najeriya, FAAN, ta samu, FAAN ta ce ba lallai bane ta iya biyan cikakken albashin ma’aikatanta.

Daily Trust ta ruwaito FAAN ta ce ma’aikata za su fuskanci canji a albashinsu daga watan Mayu, amma da zarar jirage sun cigaba da tashi za ta cigaba da biyansu cikakkun hakkokinsu.

KU KARANTA: Dan tsaro ba tsoro ba: Gwamnati ta girke zaratan Sojoji masu jiran ko-ta-kwana a jahar Filato

Hukumar FAAN ta shiga matsalar albashi ne tun bayan da aka dakatar da sauka da tashin jirage a Najeriya a wani mataki na dakile yaduwar cutar Coronavirus tun a watan Afrilu.

Rashin zirga zirgan jiragen yasa aka samu nakasu a kudaden shigar hukumar, don haka a ranar 19 ga watan Mayu ta sanar da ma’aikatanta halin da ake ciki.

Coronavirus: Hukumar gwamnatin tarayya ta zaftare kashi 50 na albashin ma’aikatanta
Hukumar FAAN Hoto: ThisDaylive
Asali: UGC

Shugaban FAAN, M.D Musa ne ya sanya hannu kan takardar sanarwar, inda ya shaida cewa za’a samu nakasu a albashi, amma idan komai ya daidaita, FAAN za ta biya cikon albashin.

“Sanarwa game da albashin ma’aikata, mun dauki wannan mataki ne don tabbatar da cigaba da gudanarwar hukumar, kananan ma’aikata za su samu kashi 100 na albashin su, amma ma’aikata daga mataki na 10 zuwa sama za’a rage kashi 30 zuwa 50 na albashin su.” Inji sanarwar.

Haka zalika kamfanonin sufurin jiragen sama da dama sun rage ma’aikatansu, inda wasu sun sallami kashi 80 na ma’aikatansu, wasu kuma sun baiwa ma’aikatan hutun dole.

Ita ma hukumar kula da sararin samaniyar Najeriya, NAMA, ta gudanar da taro da wakilan kungiyoyin ma’aikatanta don tattauna yiwuwar zaftare rabin albashin su a watan Mayu.

Sai dai rahotanni sun bayyana kungiyoyi guda uku sun nuna tirjiya da wannan bukata na hukumar, don haka za’a cigaba da zaman tattaunawa har a cimma a matsaya.

A wani labari, Ministan kiwon lafiya a gwamnatin Buhari, Osagie Ehanire ya ce gwamnati na damu kwarai da yadda manyan mutane masu ilimi ke mutuwa dalilin cutar Coronavirus.

Ministan ya bayyana dalilin hakan, inda yace masu kudin sun gwammace a kula dasu a gidajensu a kan su tafi cibiyoyin kulawa da masu cutar, sai lamari ya baci ake kai su asibiti.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng