Ana Shirin Nada Sababbin Ministoci, El-Rufai Ya Dankaro Shagube a Shafin Twitter

Ana Shirin Nada Sababbin Ministoci, El-Rufai Ya Dankaro Shagube a Shafin Twitter

  • Yau za a nada sababbin Ministocin Najeriya, Nasir El-Rufai ya yi maganar farko a shafin Twitter
  • Tsohon Gwamnan Kaduna ya dawo shafin da karfinsa, ya tsakuro wata tsohuwar wakar Bob Marley
  • Kusan dai za a iya cewa El-Rufai ya na shagube ne ga duk wanda ya tsargu bayan abin da ya faru

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Dublin - A karon farko a cikin makonni uku, Nasir El-Rufai, ya tuna da shafinsa na X wanda mutane su ka fi sani da Twitter.

Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya bayyana a dandalin sada zumuntan a ranar Lahadi, ya saki kalamai masu harshen damo.

Malam Nasir El-Rufai wanda aka ki tantacewa ya zama minista ya tuna da wata waka da Bob Marley ya rera a lokacin rayuwarsa.

Shehu Sani/Nasir El-Rufai
Shehu Sani da Nasir El-Rufai Hoto: Shehu Sani/Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

El-Rufai ya dauko wakar shekara 47

Kara karanta wannan

A'a ba laifinmu ba ne: Sanata Ya Fadi Wadanda Su Ka Hana El-Rufai Zama Minista

A daidai lokacin da za a rantsar da sababbin ministoci a yau, sai aka ji ‘dan siyasar ya dauko wannan waka ta ‘Who The Cap Fit’.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wakar fitaccen mawakin wanda ya rayu tsakanin 1966 da 1981 a Jamaika, za a ji yadda ya ke bayanin rashin adalcin ‘dan adam.

"Mutum da mutum babu adalci, yara/Ba ka san wa za ka yarda da shi ba/Babban makiyinka zai iya zama babban abokinka/
Kuma babban abokinka, ya zama babban makiyi/Wasu za su ci kuma su sha tare da kai."

- Bob Marley

Malam El-Rufai ya dawo Twitter

Wannan waka da aka rera da Ingilishi a 1976 ta yi magana a kan munafukai, ta na mai nuna cewa duk wanda ya tsargu, da shi ake magana.

Kafin nan Nasir El-Rufai ya dauko wani gajeren labarin abin da ya faru tsakanin Deng Xiaoping da jikinsa, Mao Zedong a wajen Chairman Mao.

Kara karanta wannan

Sheikh Ahmad Gumi Ya Tona Masu Karkatar da Shugaba Tinubu da Muguwar Shawara

An kawo labarin tsohon shugaban na Sin ne domin tallata tsarin jari hujja kan manufar gurguzu. Kafin nan Malam ya yabi gwamnatin Tinubu.

Kafin a je ko ina aka ji Sanata Shehu Sani a shafinsa ya na wani abin mai kamar martani, ya na cewa:

"Na maida shi ya zama mawakin Reggae da Rastafarian.’

- Shehu Sani

Kwankwaso da Atiku sun hadu

Ku na da labari Rabiu Musa Kwankwaso ya karbi bakuncin tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar a gidansa da ke garin Abuja.

Yayin da Abdullahi Ganduje ya hadu da Nyesom Wike, Atiku ya hadu da madugun Kwankwasiyya, hakan ya bar masu nazarin siyasa da dogon tunani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng