Sheikh Ahmad Gumi Ya Fadi Wadanda ke Karkatar da Tinubu da Muguwar Shawara

Sheikh Ahmad Gumi Ya Fadi Wadanda ke Karkatar da Tinubu da Muguwar Shawara

  • Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya koka game da halin tattalin arzikin da al’umma ta ke ciki
  • Shehin malamin musuluncin bai goyon bayan Bola Tinubu a kan janye tsarin tallafin man fetur
  • Fakihin ya zargi na kusa da Tinubu da zuga shi wajen gallazawa jama’a, ya wanke shugaban kasar

Abuja - Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi tsokaci a game da gwamnati mai-ci a Najeriya a karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu.

Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi a wani karatu da yake yi a masallacin Sultan Bello a Kaduna, ya yi magana kan halin da ake ciki.

Kamar yadda mu ka ci karo da wani fai-fai a dandalin Twitter, babban malamin fikihun ya bada labarin yadda miyagu su ka koma satar fetur.

Sheikh Ahmad Gumi
Ahmad Gumi da Bola Tinubu Hoto: thewhistleng da thegazelle.org
Asali: UGC

Ayi hattara da barayin fetur - Gemu

Kara karanta wannan

Sanatan APC Ya Tona Yanayin da Tinubu Ya Iske Tattalin Arziki a Hannun Buhari

A cewarsa, ‘yan bindiga sun shiga gidan man wani abokinsa ‘dan kasuwa cikin dare, su ka sace fetur daga tanka bayan hallaka direban motar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Malamin ya gamsu da abin da limamin masallacin ya fada, ya ce talaucin da ake ciki zai iya jawo a fisge ledar cefane daga hannun mutum.

Sheikh Ahmad Gumi ya yi nuni ga wani daga cikin Sarakan Arewa, ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta na daukar shawarwarin da su ke badawa ne.

A ra’ayin tsohon sojan, masu wannan kira ba asalin masana tattali ba ne, masu ra’ayin turawan yamma ne da ke goyon bayan a cire tallafi.

Tinubu zai tara kudi a hallaka jama'a

"Wai me su ke so su tara kudi su hallaka al’umma? Shi Bola Tinubu ba wai ina zarginsa da cewa irin maketacin da ba ne.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Karin Bayani a Kan Yiwuwar Dawo da Tallafin Man Fetur

Amma ya na cikin batattu, bai cikin wadanda Allah (SWT) ya yi fushi da su, batar da shi aka yi, wadanda su ke fito da shi.
Ba ku ganin Sarakunanmu, wani ya fito ya ce shi masanin tattalin arziki ne, a cire kaza da kaza.
Wadannan su ke bi, su kuma ba masanin tattali ba ne, su su ke saurare, shi kuma zai rika ganinsu kamar wasu manyan Arewa.
Shi kuma bai san wadancan Turawa ba ne. Wace kas ace ba ta tallafi? Ita Soviet gaba daya kasar ma tallafi ce, haka Sin?"

- Ahmad Abubakar Mahmud Gumi

Za a dawo da tallafin fetur?

Fadar shugaban Najeriya ta ce tsarin tallafin fetur da aka yi waje da shi a Mayu ya tafi kenan, an ji labari babu wani shirin maido kowane nau’i na tallafi.

Bola Tinubu ya gamsu za a iya cigaba da saida fetur a kan farashin da yake ba tare da an dawo da hannun agogo baya kamar yadda wasu su ke tunani ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel