Mayakan Boko Haram Sun Kama Kwamandojin ISWAP 3 Da Wasu Fiye Da 50 A Jihar Borno

Mayakan Boko Haram Sun Kama Kwamandojin ISWAP 3 Da Wasu Fiye Da 50 A Jihar Borno

  • 'Yan ta'addan Boko Haram sun kama mayakan ISWAP 60 a wani samame da suka kai a maboyarsu
  • Yayin farmakin, 'yan Boko Haram din sun kuma cafke manya-manyan kwamandojin kungiyar guda uku
  • Wadanda aka kaman daga bisani an rufe su a karkashin kasa na Kwatan Mota a matsayin fursunonin yaki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Borno - Mayakan Boko Haram sun cafke 'yan kungiyar ISWAP 60 da suka hada da kwamandojinsu uku a jihar Borno.

An bayyana kwamandojin da suna Abubakar Saddiq da Malam Idris da kuma Abou Maimuna.

Boko Haram sun kama 'yan ISWAP 60 a jihar Borno
Mayakan Boko Haram Sun Cafke Kwamnadojin ISWAP 3 Da A Borno. Hoto: Tribune.
Asali: Twitter

Boko Haram sun cafke 'yan ISWAP

Zagazola Makama ya tabbatar cewa an kama 'yan ta'addan ISWAP din ne a kan hanyarsu ta zuwa Damasak da ke jihar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Yaran El-Rufai Sun Lallaba Sun Roki Shugaban Kasa ya Ba Shi Kujerar Minista

Ya ce Boko Haram a kwanakin nan su na cin nasara a kan ISWAP bayan kwace wasu daga cikin maboyarsu.

Wanda hakan ya saka su dole neman mafaka a yankin Kwatan Mota da Madayi da kuma Kukawa.

A cewar rahoton:

"Nasarar da Boko Haram ke samu a yanzu bai rasa nasaba da yadda 'yan ISWAP din ke koma wa bangaren Buduma na Boko Haram.
"Wadanda aka kaman daga bisani an rufe su a karkashin kasa na Kwatan Mota kusa da Dogon Chukwu a matsayin fursunonin yaki."

Boko Haram sun mika wuya ga sojoji

Arangamar da bangarorin biyu suka yi shi ne wanda ya afku a ranar Litinin 16 ga watan Agusta, cewar Daily Trust.

Har ila yau, mayakan Boko Haram fiye da 70 sun mika wuya tare da ajiye makamansu ga rundunar soji ta 'Operation Hadin Kai' da ke karamar hukumar Monguno.

Mayakan sun mika wuyan ne tare da iyalansu saboda irin farmaki da sojojin ke kai musu ba kakkautawa.

Kara karanta wannan

An Kuma: 'Yan Bindiga Sun Sace Wasu 7 Da Dan Mashahurin Sarki A Jihar Arewa, Sun Yi Ajalin Mutum 1

Sauran dalilan sun hada da yadda su ke fada da mayakan ISWAP wanda hakan ya yi sanadin mutuwar 'yan ta'adda 100 cikin kwanaki bakwai.

Sojoji Sun Hallaka 'Yan ISWAP Da Dama A Borno

A wani labarin, rundunar sojin Najeriya ta yi luguden wuta kan mayakan ISWAP da ke wata haramtacciyar kasuwa a karamar hukumar Bama a jihar Borno.

An kai harin ne bayan samun bayanan sirri cewa mayakan na cike a cikin kasuwar inda rundunar ta yi nasarar hallaka 'yan ta'addan da dama a yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel