Yanzu yanzu: Yan bindiga sun sake kai sabon hari a Kaduna, sun kashe mutane da dama
Rahotannin da Legt.ng Hausa ke samu yanzu na nuni da cewa wasu da ake kyautata zaton cewa 'yan bindiga ne sun kai sabon hari a karamar hukumar Kajuru, jihar Kaduna, inda suka kashe mutane da dama.
Wani mazaunin garin, wanda ya tabbbatar da faruwar kai harin, ya shaidawa jaridar TheCable cewa da yawa daga cikin wadanda harin ya shafa sun fito ne daga kauyen Karmai a gundumar Maro da ke cikin karamar hukumar.
Cikakken labarin yana zuwa...
KARANTA WANNAN: Da duminsa: Saraki ya yi korafi kan shan kaye amma ya taya wadanda suka yi nasara murna
A baya Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa, adadin wadanda suka rasa rayukansu a harin da aka kai karamar Kajuru ta jihar Kaduna ya kai mutum 130.
A makwanni biyu da suka gabata, Mr El-Rufai ya sanar da cewa, wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum 66 a harin da aka kai karamar hukumar Kajuru kwanakin baya, sai dai daga baya ya ce yawan wadanda suka mutu ya karu kwarai da gaske.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng