Malaman Addinin Islama Sun Roki Majalisa Ta Ki Amincewa El-Rufai a Matsayin Ministan Tinubu

Malaman Addinin Islama Sun Roki Majalisa Ta Ki Amincewa El-Rufai a Matsayin Ministan Tinubu

  • Kungiyar addinin Islama ta roki a cire sunan Malam Nasiru El-Rufai daga jerin ministocin da za su yi aiki da shuagba Bola Ahmad Tinubu
  • Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake kokarin fara tantance ministocin da Tinubu ya aika majalisar kasar nan a makon jiya
  • A baya El-Rufai ya bayyana kyamar sake karbar kujerar minista a kasar nan duba da yadda a baya ya yi aiki a matsayin minista

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Bauchi - Gamayyar kungiyar malamai mahaddata Alkur’ani da makaranta ta bukaci majalisar dattawa da ta ki amincewa da cancantar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a ministocin Tinubu.

Sunan tsohon gwamnan na cikin mutane 28 da shugaban kasa Bola Tinubu ya mika wa majalisar dattawa domin tantancewa da tabbatar da su a majalisar ministocinsa.

Kara karanta wannan

Bidiyon Tinubu Yana Rokon El-Rufai a Fili, Ya Karbi Mukami Idan An Kafa Gwamnati

Amma a wani taron manema labarai a Bauchi ranar Lahadi, Daraktan Ilimi na gidauniyar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Sheikh Sidi Ali, ya roki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya cire sunan El-Rufai a jerin sunayen.

Malamai sun nemi a hana El-Rufai kujerar Minista
Malam Nasiru El-Rufai, tsohon gwamnan Kaduna | dailytrust.com
Asali: Facebook

Dalilin yin wannan kira na kungiyar malamai

Ya ce nada El-Rufa’i a matsayin minista abin kyama ne ga tsagwaron adalci, daidaito da kuma sanin ya kamata, ya tsaya kekam cewa a cire sunan El-Rufai domin tabbatar da adalci, zaman lafiya, zaman lafiya da ci gaban kasa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai, shi kansa El-Rufai ya bayyana a baya cewa, ba zai so a sake ba shi kujerar minista ba saboda wasu dalilan da ya bayyana.

El-Rufai ba zai so a ba shi minista ba

A wannan karo bayan bayanai daga kungiyar, ya zuwa yanzu dai ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun El-Rufai ba, Muyiwa Adekeye.

Kara karanta wannan

Fitaccen Malamin Addini Ya Yi Gagarumin Hasashe Game Da Ministocin Shugaban Kasa Tinubu

Shin cire El-Rufai daga jerin ministocin Tinubu zai rage wani armashi daga yadda gwamnatin shugaban kasan zai kasance a tsawon shekarun wa’adinsa?

'Yan faucen waya sun shiga majalisa, ana ta sace wayoyin sanatocin Najeriya

A wani labarin, Godswill Akpabio, shugaban majalisar dattawa ya koka kan yadda ‘yan baranda ke yawan shiga harabar majalisa tare da sace wayoyin sanatoci.

Ya bayyana cewa, ana samun mutane da basu cancanta da shiga harabar ba su na shiga suna barnar illata sanatocin kasar.

Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin ganawa da wata tawagar ma’aikatan majalisar da suka kai masa ziyarar ban girma, Vanguard ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel