An Kwamushe Alkali Ya Na Rubutawa Budurwarsa Jarrabawa, An Tasa Keyarsa Zuwa Gidan Kaso

An Kwamushe Alkali Ya Na Rubutawa Budurwarsa Jarrabawa, An Tasa Keyarsa Zuwa Gidan Kaso

  • Rikita-rikita yayin da aka kwamushe alkali bayan kama shi da zargin rubutawa budurwarsa jarrabawa
  • Wanda ake zargin mai suna Semwogerere Ammaari Musa ya yi shigar mata don aikata hakan dakin jarrabawa a Uganda
  • Kafin aikata hakan, an nada Musa karamin alkali a watan Yuni na wannan shekarar tare da wasu 86 da Hukumar Shari'a ta yi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

An garkame wani alkali bayan samunsa da laifin rubutawa budurwarsa jarrabawa a kasar Uganda.

Wanda ake zargin Semwogerere Ammaari Musa, an kama shi ne a Cibiyar Lauyoyi (LCD) a Uganda, Legit.ng ta tattaro.

Alkali ya shiga hannu bayan kama shi ya na rubuta jarrabawa ga budurwarsa
Alkalin Semwogerere Ya Yi Sojan Gona Inda Ya Rubutawa Budurwarsa Jarrabawa. Hoto: Pinterest.
Asali: UGC

Semwogerere da aka nada shi a matsayin alkali a watan Yuni na shekarar 2023, ya yi shigar mata tare da rubutawa budurwarsa mai suna Irene Mutonyi jarrabawa.

Yadda Semwogerere ya shiga hannu bayan aikata lafin

Semwogerere ya shiga hannu a ranar Juma’a 28 ga watan Yuli makwanni kadan bayan Mista Semwogerere ya samu karin girma zuwa karamin alkali a Hukumar Shari’a ta kasar.

Kara karanta wannan

Bidiyon Tinubu Yana Rokon El-Rufai a Fili, Ya Karbi Mukami Idan An Kafa Gwamnati

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake magana akan lamarin, Daraktan LCD, Frank Nigel ya ce sun kai rahoton lamarin ofishin ‘yan sanda kuma ana zargin shi da laifuka biyu, cewar Aminiya.

Ya ce:

"Mun kai rahoton ofishin 'yan sanda kuma ana zargin shi da laifuka biyu na mallakar takardun bogi da kuma sojan gona.
"Za a ci gaba da tsare shi a gidan kaso har zuwa ranar 8 ga watan Agusta, za mu tabbatar an yi masa hukuncin da ya dace da ma sauran masu laifi.
"LCD yanzu ta na gudanar da jarrabawar karshe ne a cibiyar kuma ba za mu lamunci satar jarrabawa ba ta ko wani bangare, za mu ci gaba da tsarin mu na tabbatar da cewa an bi doka."

Hukumar shari'a ta fitar da sanarwa akan Ammaari

Hukumar Shari'a ta kasar Uganda ta bayyana a shafin Twitter cewa an rusa nadin da aka masa a matsayin alkali.

Kara karanta wannan

Innalillah: 'Yan bindiga sun kashe babban malamin Izala da wasu 5 a jihar Kaduna

Cewar sanarwar:

"Semwogerere Ammaari Musa an nada shi karamin alkali a ranar 12 ga watan Yuni tare da wasu 86, Ammaari ba zai kasance tare da sauran alkalan da aka nada su tare ba."

An Maka 'Group Admin' A Kotu Kan Zargin Cire Mamba A Rukunin 'WhatsApp', An Kara Masa Girma

A wani labarin, an maka 'Group Admin' a kotu bayan ya cire mamba a rukunin 'WhatsApp' na taimakon al'umma.

Wanda ke karar mai suna Herbert Baitwababo ya tabbatarwa da kotu cewa ba a yi masa adalci ba da aka cire shi a 'Group' din.

Ya bayyana cewa har kudi ya biya saboda ya kasance mamba a rukunin da aka kirkira don marasa karfi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel