Nasarawa za ta ba Dangote fili domin aikin shinkafa da fulawa – Inji Sule
Mun samu labari cewa nan gaba kadan ake sa rai gwamnatin jihar Nasarawa da Kamfanin Dangote za su sa hannu a yarjejeniyar gina kamfanin fulawa da casar shinkafa da noman rogo.
Mai girma Abdullahi Sule ya bayyana gwamnatinsa ta kammala shirin aika Tawagar jami’an ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu zuwa Legas domin a sa hannu a yarjejeniyar.
Gwamna Abdullahi Sule ya ce a wannan shiri, kamfanin Dangote zai samu katafaren fili har eka 50, 000 domin kafa gona da kamfanin shinkafa a cikin kananan hukumomin Doma da Nasarawa.
Abdullahi Sule ya kara da cewa kamfanin fulawa da za a gina a jihar zai ci eka 10, 000 na fili, inda za a rika aikin rogo. Za a bude wannan katafaren kamfani ne a cikin karamar hukumar Wamba.
KU KARANTA: Gwamnatin Najeriya za ta karrama Dangote da wasu mutum 25
Manema labarai sun rahoto cewa gwamnan ya yi duk wannan bayani ne a lokacin da ya karbi bakuncin Kansiloli na duka kananan hukumomi jihar da su ka ziyarce sa a gidan gwamnati.
Sule ya jawo hankalin Kansilolin da ke mulki a jihar da su yi kokarin kawo sababbin dabarun yadda za su samu kudin shiga. Gwamnan ya ce wannan zai taimaka masu wajen rike kansu.
“Ina kalubalantar ku da ku nemi hanyar tatso kudi, ku yi wasu ayyuka daban da biyan albashi. Ba zai yiwu mu na kokarin nemo kudi a matsayin jiha, amma duk su kare kan albashi ba.”
Gwamnan da ya dare kan karagar mulki watanni shida da su ka wuce, ya ja-kunnen masu mulkin da su rika tabuka wasu ayyuka, ba kurum su biya ma’aikata su kalmashe hannuwa ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng