Juyin Mulki: Ali Nuhu Ya Taya Al'ummar Nijar Alhinin Halin Da Suke Ciki

Juyin Mulki: Ali Nuhu Ya Taya Al'ummar Nijar Alhinin Halin Da Suke Ciki

  • Fitaccen jarumin Kannywood, Ali Nuhu ya taya daukacin al'ummar Nijar alhinin halin da suka riski kansu a ciki a hannun dakarun tsaro
  • Jarumi Ali Nuhu ya yi wa Shugaba Mohammed Bazoum fatan alkhairi yayin da sojoji suka hambarar da gwamnatinsa
  • A wata sanarwa da su ka fitar ta bakin Kanal Amadou Abdramane, sojojin sun sanar da cewa sun kawo karshen gwamnati mai-ci a kasar Nijar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Fitaccen jarumin masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Ali Nuhu, wanda aka fi sani da Sarkin Kannywood ya yi tsokaci a kan halin da Jumhuriyar Nijar ke ciki sakamakon hambarar da gwamnatin farar hula da sojojin kasar suka yi.

Sarki Ali ya taya daukacin al'ummar kasar alhinin wannan yanayi da suka riski kansu a ciki na juyin mulki a wannan karni na 21.

Kara karanta wannan

Magana ta Ƙare: Sojoji Sun Sanar da Hambarar da Bazoum a Juyin Mulkin Nijar

Ali Nuhu ya yi wa Bazoum fatan alkhairi yayin da sojoji suka hambarar da gwamnatinsa
Juyin Mulki: Ali Nuhu Ya Taya Al'ummar Nijar Alhinin Halin Da Suke Ciki Hoto: Premium Times
Asali: UGC

A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook, jarumin ya roki Allah da ya kawowa al'ummar Nijar na gida da waje saukin wannan al'amari.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Har ila yau, ya roki Allah ya baiwa shugaban kasar da aka hambarar da gwamnatinsa, Mohammed Bazoum juriyar cin wannan jarrabawa sannan ya kuma kare shi.

Ya wallafa a shafin nasa:

"Ina taya daukacin al’ummar jamhuriyyar Niger na gida da waje alhinin abin da ke faruwa. Allah ya kawo musu sauki. Allah ya bawa Shugaban kasa Bazoum juriya da kuma kariya. Ameen."

Martanin jama'a a kan kifar da gwamnatin farar hula da sojojin Nijar suka yi

Muhammadu Aminu ya yi martani:

"Gaskiya kam sunyi Babban kuskure Na suka kifar da Gwabnatin shugaba Bazou kuma Insha Allahu sai sunyi Danasanin yin Haka, saidai yakamata Libiya da Iraqi su zama Babban Darasi garesu."

Kara karanta wannan

Assha: Wata Amarya Ta Datse Mazaƙutar Angonta Kan Abu 1 a Jihar Katsina

Zayyanu Abubakar Sagagi ya ce:

"Maganar gaskiya Ina goyon baya Sojojin Niger Duk Dan Kasa nagari bayason tashin hankali musamman halin rashin tsaro gayan ta'adda nakashi jama'a badare barana Jama'a mutsaya muyi nazarifa Maganar Gaskiya."

Muhammadu Aminu ya yi martani:

"Gaskiya kam sunyi Babban kuskure Na suka kifar da Gwabnatin shugaba Bazou kuma Insha Allahu sai sunyi Danasanin yin Haka, saidai yakamata Libiya da Iraqi su zama Babban Darasi garesu."

Abdulganiyu Usman Bafeto ya ce:

"Laifin bazoum kawai shine yanaso ya ciresu daga qangin bautan faransa."

Umar Ya'u Kubau ya yi martani:

"Ai ta riga tabbata. Sai dai Allah Ya wanzar da zaman lafiya a kasar."

Isa Brown ya yi martani:

"Amen ya allah.
"A zahiri dai babu wani Abu da shugaba Bazoum yayiwa al'ummar kasar Niger , kawai makir cine irin na kasar France kan manufar ta wanda shi bazoum din yaki aminta dasu."

Sojoji Sun Sanar da Hambarar da Bazoum a Juyin Mulkin Nijar

Kara karanta wannan

"Tsohon Shugaban Majalisa Ya Jawowa Abdullahi Adamu Rasa Shugabacin APC"

A baya mun ji cewa, an cire Mohammed Bazoum daga kan karagar mulki a Nijar ta hanyar wani danyen juyin mulki da aka gudanar a ranar Larabar nan.

Rahoton da mu ka samu daga Reuters ya tabbatar da cewa wasu sojoji sun yi wa gwamnati tawage sun kifar da Shugaba Mohammed Bazoum.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng