Akwai Riba Sosai: Yar Najeriya Da Ke Aiki a UK Ta Fadi Yawan Kudin da Take Samu a Bidiyo

Akwai Riba Sosai: Yar Najeriya Da Ke Aiki a UK Ta Fadi Yawan Kudin da Take Samu a Bidiyo

  • Wata hazikar yar Najeriya da ke zama a UK ta bayyana yawan kudin da take samu daga aikin kula da mutum
  • A cewar matashiyar, ana biyanta fam 100 a kullun kan aikin kula da mutum da take yi a Turai
  • A wani bidiyo da ta saki, ta yi jawabinta ne ga masu cin zarafi da ke mata ba'a kan aikin da take yi a Birtaniya

Birtaniya - Wata matashiyar budurwa yar Najeriya da ke zama a Birtaniya, Ihemeson Akunna, ta bayyana yawan kudin da take samu a matsayin mai aikin kula da mutum a kasar.

Ta wallafa wani bidiyo a shafinta na TikTok, tana mai bayyana yadda ake biyanta a kullun saboda yin wannan aiki.

Matashiya
Akwai Riba Sosai: Yar Najeriya Da Ke Aikin Kula da Mutum a UK Ta Fadi Yawan Kudin da Take Samu a Bidiyo Hoto: @juliaglam2/TikTok
Asali: UGC

A cewarta, tana samun fam 100 (N56,163) a kullun kan wannan aiki, kuma tana matukar alfahari da neman ta.

Kara karanta wannan

Sai a kula: Kudaden bogi na kara yawa, mai POS ya ba da N1000 na bogi, an ki karba a kasuwa

Bidiyon ya haifar da martani da dama daga mutane masu sha'awar samun irin wannan makudan kudi a Turai.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kalamanta:

"Aikin kula da mutum ta ke yi a UK. Ko duba nawa fam 100 yake a naira, abun da muke samu kenan a rana 1."

Jama'a sun yi martani

@AsaYoung ta rubuta:

"Kara fada da karfi £136 a kullun ba wasa bane. Aikin kula da mutum nan muka kwana. Kirsimeti da sabuwar shekara ana rubanyawa sau biyu ne."

@amarachimadudonu ta yi martani:

"Magana ta gaskiya! Da haraji ko babu haraji £100 a rana yana da yawa. Koda £50 a rana ne ya yi."

@Nonyflexy ta kara:

"Ki je ki yi aikin kula da mutum a Australia ki gode mun daga baya."

@cozybae ta yi martani:

"Dan Allah ina bukatar aiki...ba da sauki ake samun aikin ba ma, wasun mu na zaune ne a nan babu aikin yi lol."

Kara karanta wannan

Yadda Budurwa Ta Sauya Ta Koma Hadaddiyar Bebi Watanni 3 Bayan Komawarta UK, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

@Nwankwo Chidiebube ya yi martani:

"Ba su san me ke gudana ba."

@PascalineGabriella ta rubuta:

"Yar'uwa ina taya ki murna kada ki kula da abun da mutane ke cewa, ina sha'awar aikin kula da mutum. Dan Allah ta yaya zan nemi aikin."

Gwarzon kwallon kafa ya samu kyautar kwai

A wani lamari mai ban mamaki a kasar Zambiya, an ba wani zakaran gasar buga kwallon kafa kyautar kwai.

Matashin ya samu kiretan kwai biyar bayan ya zura kwallo daya tilo a aka ci a wasar a raga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel