Ba Dadi: Wata Amarya Ta Gutsire Mazaƙutar Angonta a Jihar Katsina

Ba Dadi: Wata Amarya Ta Gutsire Mazaƙutar Angonta a Jihar Katsina

  • Rundunar yan sanda ta kama wata Amarya bisa zargin guntule mazaƙutar Angonta a karamar hukumar Ƙafur ta jihar Katsina
  • Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, ASP Abubakar Aliyu, ya ce a halin yanzu Angon na kwance a Asibitin Malumfashi
  • Ya ce hukumar zata gurfanar da matar gaban Kotu da zaran ta karkare bincike kan abinda ya faru

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Katsina state - Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Katsina, ta tabbatar da cafke wata amarya mai suna Tinene Isa, bisa zargin yanke mazaƙutar mijinta.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, ASP Abubakar Aliyu, ya tabbatar da kamen a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ranar Laraba a Katsina.

An kama Amaryar da ta yanke mazakutar Angonta a Katsina.
Ba Dadi: Wata Amarya Ta Gutsire Mazaƙutar Angonta a Jihar Katsina Hoto: Policeng
Asali: Facebook

ASP Aliyu ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a karamar hukumar Kafur da ke cikin jihar Katsina, Arewa maso Yammacin Najeriya, kamar yadda jaridar daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

DSS Sun Cafke Shugaban NSPMC da NIRSAL da ya yi takarar Gwamnan Katsina

Kakakin yan sandan bai faɗi sunan Angon da wannan lamari ya faru da shi ba amma ya ce a halin yanzu yana kwance a babban Asibitin Malumfashi ana kulawa da shi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kuma yi bayanin cewa Amaryar da ake zargi da aikata wannan ɗanyen aiki, ta yi amfani da reza mai kaifi wajen gutsire wa Angonta mazaƙutarsa.

A kalamansa, jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan Katsina ya ce:

“Na gaya muku, muna kan gudanar da bincike kan lamarin ne a halin yanzu. Amarya ce kuma ta haura shekara 30 a duniya.
"Watakila ta dauki lokaci mai tsawo kafin ta yi aure, ko kuma wannan ba shi ne aurenta na farko ba."
"Ba ni da cikakken bayani, za mu gano duk wadannan da sauran bayanai a bincikenmu."

A cewarsa, hukumar 'yan sanda zata gurfanar da wacce ake zargi a gaban kotu da zaran an kammala bincike kan ainihin abinda ya faru, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Wike: Muhimman Abubuwa 5 Da Ba Ku Sani Ba Gameda Ministan Tinubu Na Birnin Tarayya

"Ba Zan Karɓa Ba Sai Kin Duƙa" Miji Ya Umarci Matarsa a Bidiyo, Ya Ki Karban Abinci

A wani labarin na daban Wata mata 'yar Najeriya ta sha mamaki yayin da habibinta ya umarci ta duƙa kan guiwa kafin ya karɓi abincin da ta kawo masa.

Ma'auratan sun sha dirama kan haka a wani gajeren bidiyo da aka wallafa a shafin sada zumunta, mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel