Sheikh Idris Abdulazeez Zai Ci Gaba da Zaman Gidan Kaso Saboda Tsaikon da Aka Samu a Belinsa

Sheikh Idris Abdulazeez Zai Ci Gaba da Zaman Gidan Kaso Saboda Tsaikon da Aka Samu a Belinsa

  • Rahoton da muke samu ya bayyana yadda aka ci gaba da tsare babban malamin jihar Bauchi kan zarge-zarge da yawa
  • An ce malamin zai ci gaba da zaman gidan kaso duk da kuwa ya samu beli a baya, yanzu kuma aka ce ya samu tsaio
  • Ya zuwa yanzu, an umarci kotun muslunci ta mayar da bayanan shari’ar zuwa kotun tarayya da ke zamanta a jihar Bauchi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Bauchi - Fitaccen malamin addinin Islama a Bauchi, Dakta Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, zai ci gaba da zaman gidan dan kande bayan sake jinkirta belinsa saboda wani tsaiko.

A ranar Laraba ne kotun ta sake zamanta bayan shafe kwanaki 30 tana tsare da malamin a gidan yarin Bauchi.

Lauyoyin wanda ake tuhuma karkashin jagorancin Barista Abubakar Sadiq, sun shaida cewa kotun ba ta da hurumin ci gaba da zaman shari’ar kasancewar an dage karar zuwa babbar kotun tarayya ta 7 da ke Bauchi.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Fitaccen Ƙwararren Likita Yana Kan Aiki a Arewacin Najeriya

Za a sake tura Sheikh Idris zuwa magarkama
Sheikh Idris Abdulazeez Dutsen Tanshi | Hoto: aminiya.ng
Asali: UGC

Bai dace a yi shari’ar a kotun muslunci ba

Bayan tattauna batutuwan da suka shafi belin babban malamin, alkalin kotun Malam Hussaini Turaki, ya bayar da belinsa bisa wasu sharudda uku, Aminiya ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An naqalto cewa, bayan tattauna batun belinsa, Malam Hussaini Turaki, alkalin kotun ya ba da belinsa kan wasu sharudda guda uku.

Yadda batun zuwansa kotu ya fara

An ruwaito cewa, an tsare Sheikh Abdulaziz ne a ranar 15 ga watan Mayun 2023 bisa tuhumarsa da tada hankalin jama’a a karatunsa.

Haka kuma ana zarginsa da yin kalaman batanci ga ma’aiki wanda kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, CP Alhassan Aminu ya gurfanar da shi a gaban kotu kan hakan.

Kotu ta sake tura fitaccen malamin addinin Musulunci zuwa gidan yari tsawon wata 1

A wani labarin, Babbar Kotun Musulunci mai zama a jihar Bauchi, ta sake tura fitaccen Malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Dakta Idris Abdul’aziz, gidan yari tsawon wata daya.

Kara karanta wannan

Yadda Marigayi Albani Ya Hango Janye Tallafin Man Fetur Shekaru 9 da Suka Wuce

Rahoton Aminiya ya nuna cewa Kotun ta sake bada umarnin tsare babban limamin Masallacin Dutsen Tanshi a kurkuku ne bisa zargin ya, "Raina kotu."

Alkalin Kotun, mai shari'a Malam Hussaini Turaki, ne ya yanke wannan hukuncin yayin zaman sauraron ƙarar ranar Litinin, 19 ga watan Yuni, 2023.

Hukuncin alkalin na nufin Sheikh Idris Abdul'aziz, zai ci gaba da zama a Kurkuku har zuwa ranar 19 ga watan Yuli, 2023 lokacin da za'a dawo domin ci gaba da sauraron ƙarar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel