Karanta domin sanin amfanin Citta 7 wanda yakamata kowa ya sani har dakai

Karanta domin sanin amfanin Citta 7 wanda yakamata kowa ya sani har dakai

- Daga yau kallon da kake yiwa Citta zai sauya idan ka karanta

- Kasashen kamar China da India suna amfani da ita sosai don sanin muhimmancinta

Ana danganta tarihin Citta dai tun karni na 13, kimanin shekaru 5000 da suka wuce, lokacin da wani masani dan kasar China mai suna Confucius ya gano irin albarkar da Cittar ta kunsa na magani da kuma sinadaran sanya kamshi a abinci ko lemo sha (Juice).

Bayan wani lokaci ne kuma aka fara busar da ita ana safararta zuwa kasashe daban-daban domin morewa da amfanuwa da ita.

Romawa yan kasar Italiya na daga cikin farkon wadanda suka rike ta amatsayin magani da sinadarin girki.

A yau a ko’ina Citta na daga cikin jerin abubuwan amfani sosai a cikin girki da abin sha (Juice), sannan kuma ana amfani da ita wajen magani matuka gaya.

A kasar India kusan kowanne shagon siyarda kayan girki suna siyar da Citta, Mutanen kasar na amfani da ita a fannoni iri-iri kuma har ta zama wani fanni a al’adunsu da magungunansu kamar wajen taimakawa gashi rashin karyewa da sauransu.

Amma ya kamata a sani cewa in dai sabuwar danyar Citta ce akayi lemo da ita baya wuce kwana daya ko biyu zai lalace sakamako tana da sinadarin alkaline wanda shi kuma baya dadewa yake baci, sai dai in an sanya lemon cikin na’urar sanyi (Fridge).

Yau Legit.ng ta kawo ku wasu daga cikn hanyoyin da zaku yi amfani da Cittar don warkarwa daga cutuka da sauran damuwa.

Narkar da abinci cikin sauri

Shin ko kasan amfanin Citta 7 da ya kamata kowa ya sani
Shin ko kasan amfanin Citta 7 da ya kamata kowa ya sani

Shin ko kasan cewa cikin mutum na aiki ne kamar injin markade? To haka batun yake, wasu lokutan mutane kanci abubuwan da suke da wahalar narkewa a ciki, amma da taimakon lemon Cittar da aka hada shi da lemon tsami da dan gishiri asha kafin ko bayan cin abinci, kan taimaka sosai wajen saukaka narkewar abincin da muka ci.

KU KARANTA: Rikita-Rikita: An kashe babban malamin addini da wasu mutane 2 a wajen taron APC a Arewa

Idan kowa aka sha kafin cin abincin to zai kara sanya Mutum yaci sosai, saboda lemon yana farfadoda sha’awar cin abinci cikin lokaci kalilan.

Maganin Mura

Shin ko kasan amfanin Citta 7 da ya kamata kowa ya sani
Shin ko kasan amfanin Citta 7 da ya kamata kowa ya sani

Hausawa suka ce a rashin sani yasa Kaza ta kwana kan dami. Idan kai ko wani yana korafin majina ta dame shi a kirji ko baya iya numfashi yadda ya kamata ko kuma cikinsa ya cushe kamar ana cunkoson ababen hawa, maza bashi wanann shawarar , ya samu ya hada lemon Citta ya dan sanya Attaruhu da zuma ya sha shi da zafinsa a kalla sau biyu ko uku a rana. Ko lemonta ita kadai aka sha zai yi maganin dashewar murya.

Maganin gajiya da ciwon jiki

Shin ko kasan amfanin Citta 7 da ya kamata kowa ya sani
Shin ko kasan amfanin Citta 7 da ya kamata kowa ya sani

A kwanan baya Legit.ng ta kawo muku rahoton yadda shan Paracetamol da Ibuprofen da Mata masu ciki keyi, na iya hana zuri'arsu haihuwa nan gaba, a yanzu ga hanya sahihiya don gujewa shan kwayoyin da zasu iya illata lafiya.

Shan lemon sabuwar danyar Citta zai taimaka mutuka gaya wajen kawar da gajiya da kuma ciwon jiki domin Cittar na dauke da sinadaran dake karawa garkuwar jiki karfi.

Domin magannin ciwon baya kuwa, sai a samu lemon Citta (Juice) cikin babban cokali a hada tare da Man Zaitun a zuba wurin a rika yiwa Mutum tausa ana murzawa, dazar an farka da safe za’a nemi ciwon a rasa.

Idan kuma ciwon hakori ne, sai a sanya sabuwar danyar cittar karama a tsakanin hakori da dadashin zuwa wani lokaci. Haka zalika idan ciwon kai ne na bari daya ya addabe Mutum, sai kawai ya sha lemon (Juice) Cittar cikin cokali biyu na shayi bayan ya hada shi da zuma mai kyau.

Saisaita hawa da saukar jinni

Shin ko kasan amfanin Citta 7 da ya kamata kowa ya sani
Shin ko kasan amfanin Citta 7 da ya kamata kowa ya sani

A wani littafi ‘The Healing Herbs’ da shahararren mawallafi kan harkar lafiyar nan Michael Castleman ya rubutu, yayi bayanin abubuwa da dama da akan iya amfani da su wajen magance kananun damuwa batare da ansha kwaya ba, cikin littafin yayi bayanin Citta yadda take iya magance hawan jini da ita.

Inda ya bayyana cewa, wasu sinadarai dake cikin Citta na taimakawa wajen yakar tattaruwar mataccen jinni a cikin jiki

Shin ko kasan amfanin Citta 7 da ya kamata kowa ya sani
Shin ko kasan amfanin Citta 7 da ya kamata kowa ya sani

da kuma bubbuda hanyoyin da jinin ke wuce, wanda hakan kan taimaka matuka wajen kimanta hawa da saukar jinin Mutum.

A cewar binciken nasa, Cittar na kuma iya magance Kitsen nan mai wahalar narke da likitoci ke kashedin yawan ta’ammali da shi (Cholesterol), wand kan iya jawo cututtukan dake da alaka da zuciya.

Shin ko kasan amfanin Citta 7 da ya kamata kowa ya sani
Shin ko kasan amfanin Citta 7 da ya kamata kowa ya sani

Gyaran numfashi mai wari

Shin ko kasan amfanin Citta 7 da ya kamata kowa ya sani
Shin ko kasan amfanin Citta 7 da ya kamata kowa ya sani

Ka wanke baki amma dai har yanzu numfashinka baya burgeka wajen kamshi? To saurara ga mafita, Citta na dauke da sinadarin Vitamin C wanda zai taimaka wajen kashe duk kwayoyin cututtukan dake cikin bakin da suke jawo numfashi mara armashi.

Akan sha lemon Cittar bayan an hada shi da lemon tsami da tafashasshen ruwa a zuba a baki a kukure sosai na yan mintuna.

Maganin kurajen fuska

Shin ko kasan amfanin Citta 7 da ya kamata kowa ya sani
Shin ko kasan amfanin Citta 7 da ya kamata kowa ya sani

Kurajen fuska kan bata sha’anin da aka shirya musamma ga mata, idan akwai fita ta kece raini.

To albishirinki! Ga wata hanya da watakila baku sani ba, samu Citta kidan matso ruwanta a sanya a wajen kurajen yayi kamar mintuna biyar, sai a wanke da ruwan sanyi. Kuma ana iya yin shayin Cittar a rinka sha domin maganin kyamushasshiyar fata tayi luwai.

wani likita kwararre a harkar fata Dr. Deepali Bhardwaj, yace “shan lemon (Juice) Cittar kan iya kashe duk wasu cututtukan dake damun fata tare da kuma karfafawa fatar farfado da kyawunta, kana kuma ana iya shafawa a wurin da ya samu rauni domin shafe tabon”.

Karin gashi

Shin ko kasan amfanin Citta 7 da ya kamata kowa ya sani
Shin ko kasan amfanin Citta 7 da ya kamata kowa ya sani

Ina Mata? anzo wurin, Shan lemon (Juice) na Citta akai-akai yana sanya karfin gashi ga mata masu gashin da yake yawan karyewa.Sai dai kuma Citta na da yaji wasu basa iya shanta sosai, amma akan dan hada ta da albasa a rika shafawa a cikin fatar kai a bar shi kamar tsawon mintuna sha biyar zuwa rabin awa, kafin a wanke sannan a bar shi ya bushe sarai.

Shin ko kasan amfanin Citta 7 da ya kamata kowa ya sani kuma ana son Karin gashi, sai a rika shan kofi hudu na man Kwakwa da Tafarnuwar da aka daka kwallo uku da kuma cokali shida na madarar Kwakwa da cokali biyu na Zuma da cokali daya na lemon Cittar na taimakawa wajen kara yawan gashi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel