‘Dan shekara 29 ya Zama Likitan Gwamna, An ba ‘Dan 34 Kujerar Kwamishina a Katsina

‘Dan shekara 29 ya Zama Likitan Gwamna, An ba ‘Dan 34 Kujerar Kwamishina a Katsina

  • Dr. Abdulrahim M. Ma’aji ya zama Likitan Gwamnan jihar Katsina, yana mai kasa da shekaru 30
  • A yau kuma aka ji Gwamna Dikko Umaru Radda ya zabi ‘Dan shekara 34 ya zama Kwamishina
  • Matasa da mata sun samu mukamai har da kujeru a majalisar zartarwa a mulkin Dikko Radda

Abdulrahim M. Ma’aji ya dauki hankalin jama’a da jin labari ya zama likitan da yake kula da Gwamnan jihar Katsina.

Abin ban sha’awar shi ne duka shekarun Dr. Abdulrahim M. Ma’aji 29 a Duniya, abin da ba kasafai aka saba ji a nan ba.

Isah Miqdad, babban mai taimakawa Gwamna Dikko Umaru Radda kan harkar sadarwa na zamani, ya sanar da haka.

Gwamnan Katsina
Likitan Gwamnan Katsina Matashi ne Hoto: @Miqdad_Jnr
Asali: Twitter

Likitan Gwamna Dikko Radda

A ranar Laraba, Miqdad ya ce matashin Likitan ne mai duba Mai girma Dikko Radda.

Kara karanta wannan

An Yi Son Kai: Majalisa Za Ta Binciki Duka Mukaman da Aka Bada a Mulkin Buhari

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dr. Ma’aji mutumin karamar hukumar Ingawa ne kuma ya yi karatu ne a jami’ar Ibn Sina da ke birnin Khartoum a Sudan.

Wannan jami’a wanda a baya aka sani da ‘Khartoum College of medical sciences’ tayi suna a wajen yaye likitoci a Afrika.

Yusuf Rabiu Jirdede

A yau din ne kuma Hadimin Gwamnan ya ce an zabi Yusuf Rabiu Jirdede a cikin wadanda ake so su zama Kwamishinonin Katsina.

Shi kuwa Yusuf Jirdede wanda ya fito daga Maiadua, matashi ne mai shekara 34.

Idan har majalisa ta tantace shi a matsayin Kwamishinoni, watakila zai zama ‘dan auta a cikin majalisar zartarwa ta jihar watau SEC.

Karin Kwamishinonin Katsina

Sannan akwai wasu mata; Fadila Muhammad Dikko, Hadiza Yaradua da Zainab Musawa Musawa da aka aikawa majalisa sunayensu.

A cikin Kwamishinonin da ake so a nada akwai Dr. Faisal Umar Kaita, wanda tsohon dalibinsa, Salim Yunusa ya ce an yi dace da shi.

Kara karanta wannan

Renewed Hope ko Wahala: An fara dawowa daga rakiyar Tinubu kan tashin kudin fetur

"...Dr. Faisal Kaita: an yi dace" - Dalibinsa

Malam Salim Yunusa wanda marubuci ne a Arewacin Najeriya ya ce Dr. Faisal Kaita malami ne mai matukar basira da kuma saukin kai.

"Amma bai kaunar rashin gaskiya ko cuwa-cuwa. Malami ne da ya yi imani da kwazo kuma mai tunzura dalibansa su cin ma nasara.
Duk ma’aikatar da zai jagoranta, su shirya ganin gagarumin sauyi. Mutum ne wanda abin da yake aikatawa ya fi kalaman bakinsa.
Gwamna Radda da daukacin mutanen jihar Katsina sun yi sa’ar samun shi a gwamnati."

- Saleem Yunusa

Gwamnan Kano ya kara nadin mukamai

Rahoto ya zo cewa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida Gida ya cigaba da nade-naden mukamai.

Babban Sakataren yada labaran Gwamna, Sanusi Dawakin Tofa ya ce an ba wani matashi Dr. Dahir M. Hashim matsayi a KN-WECCMA.

Asali: Legit.ng

Online view pixel