Gwamnan Jihar Osun Ya Bayyana Ranar Laraba a Matsayin Ranar Hutu, Ya Bayar Da Dalili

Gwamnan Jihar Osun Ya Bayyana Ranar Laraba a Matsayin Ranar Hutu, Ya Bayar Da Dalili

  • Gwamna Ademola Adeleke ya bayyana ranar Laraba, 19 ga watan Yuli a matsayin ranar hutu domin murnar zagayowar shekarar Musulunci
  • Adeleke, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 18 ga watan Yuli, ya ce an bayar da hutun ne domin shigowar shekarar 1445 bayan Hijirah
  • A cewar sanarwar, gwamna Adeleke zai jagoranci wani fareti na musamman tare da al'ummar Musulmai a jihar

Osogbo, jihar Osun - Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya sanar da ranar Laraba, 19 ga watan Yuli, a matsayin ranar hutu domin murnar shigowar shekarar musulunci ta 1445 bayan Hijirah.

Kamar yadda rahoton Vanguard ya tabbatar, babban sakataren ma'aikatar cikin gida da ayyukan musamman ta jihar, Mudashiru Oyedeji, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Mummunar Gobara Ta Babbake Fadar Babban Basarake Mai Daraja a Najeriya

Gwamnan jihar Osun ya bayar da hutun shigowar shekarar Musulunci
Gwamna Adeleke ya bayyana ranar Laraba a matsayin ranar hutu a jihar Hoto: Governor Ademola Adeleke
Asali: Facebook

Oyedeji ya bayyana cewa gwamna Adeleke ya bayyana ranar Laraba a matsayin ranar hutu ne saboda ba Musulmai damar yin murnar zagayowar sabuwar shekarar Musulunci, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Gwamna Adeleke zai jagoranci fareti na musamman a jihar

Ya ƙara da cewa domin murnar zagoyowar sabuwar shekarar, gwamna Adeleke zai jagoranci wani fareti na musamman tare da Musulmai a filin wasan ƙwallon ƙafa na Osogbo, a ranar Asabar 22 ga watan Yuli.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani bangare na sanawar na cewa:

"Domin murnar zagayowar sabuwar shekarar Musulunci ta 1445 bayan Hijirah domin al'ummar Musulmin jihar Osun, gwamnan jihar Sanata Ademola Adeleke ya ayyana gobe, Laraba a matsayin ranar hutu a faɗin jihar."
"A yayin da yake taya al'ummar Musulmai murna da fatan gudanar shagulgulan zagoyowar sabuwar shekarar lafiya, gwamnan zai jagoranci wani fareti na musamman ranar Asabar a filin wasan ƙwallon ƙafa na Osogbo a cikin jerin shirye-shiryen da aka shirya domin murnar zagayowar sabuwar shekara."

Kara karanta wannan

Zulum Ya Sanya Magidanta 13,000 Farin Ciki a Jihar Borno Yayin Da Ya Yi Musu Gagarumar Kyauta

Majalisar Dokokin Jihar Osun Ta Sake Wa Jihar Suna

A wani labarin na daban kuma, majalisar dokokon jihar Osun ta sake sunan jijar daga yadda aka san shi, inda ta mayar da shi na asali wanda ake amfani da shi a baya.

Majalisar ta sauya sunan daga 'State of Osun' ya koma 'Osun State'.kamar yadda yake a baya tun asali ƙafin a sauya shi a ƙarƙashin gwamnatin da ta gabata a jihar.

Asali: Legit.ng

Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel