"Har Yanzu Abin Na Masa Ciwo Bai Samu Alfarma Ba Daga Buhari," Femi Adesina Ya Ragargaji Kukah

"Har Yanzu Abin Na Masa Ciwo Bai Samu Alfarma Ba Daga Buhari," Femi Adesina Ya Ragargaji Kukah

  • Femi Adesina, hadimin tsohon shugaban kasa, Buhari ya soki Matthew Hassan Kukah kan kalamansa
  • Kukah ya bayyana cewa cin hanci da rashawa ya yi kamari a gwamnatin Buhari fiye da ko yaushe
  • A martaninsa, Adesina ya ce Kukah na jin haushi ne Buhari ba ya shiga lamuransa lokacin mulkinsa

FCT, Abuja – Hadimin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Femi Adesina ya caccaki Matthew Hassan Kukah kan kushe gwamnatin Muhammadu Buhari.

Kukah ya kushe salon gwamnatin tsohon shugaba Buhari ne yayin bikin cikan shekaru 60 na Afe Babalola a matsayin lauya.

Femi Adesina Ya Soki Kukah Kan Zargin Cin Hanci A Gwamnatin Buhari
Tsohon Hadimin Buhari, Femi Adesina. Hoto: @FemAdesina.
Asali: Twitter

Kukah ya ce cin hanci da rashawa ya karu fiye da hankali a gwamnatin da ta shude ta Muhammadu Buhari, inda ya ce hadimin Buharin, Adesina zai tabbatar da haka, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Abba Gida-Gida Ya Mayar Da Sheikh Daurawa Kan Mukaminsa

Kukah ya bayyana yadda cin hanci ya yi yawa a lokacin Buhari

Kukah yayin taron ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Mun fuskanci mummunan yanayin cin hanci a Najeriya, Femi Adesina abokina da ke nan zai tabbatar, saboda ya yi rubutu akan abubuwan da suka faru a gwamnatin Buhari.
"Ba su suka jawo cin hanci ba, amma a gwamnatin baya, mun fuskanci mummunan yanayi na cin hanci ko ta tarbiyya ko kudi da sauransu."

Ya ba da misalin Daura, mahaifar Buhari ya ce ci gaban da ta samu ko Katsina ba su samu ba, inda ya ce shugabanni na gina karkararsu fiye da sauran wurare, cewar Daily Trust.

Femi Adesina ya mayar da martani

A nasa martanin, Femi Adesina ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa Kukah ya na jin haushi ne Buhari ba ya ta tasa, inda ya ce babu wanda zai kulasa kamar gwamnatocin baya.

Kara karanta wannan

Obasanjo, Buhari, IBB Da Lokuta 9 Da Shugaban Najeriya Ya Zama Shugaban ECOWAS

Ya ce:

"Wa zai saurari Kukah yanzu? Ya na jin haushi Buhari ba ya ta tasa kamar yadda sauran gwamnatocin baya suka yi, a lokacin da suke jin zafi, mu kuma ta na mana dadi."

Buhari Bai Yi Gudun Hijira Ba, Garba Shehu Ya Yi Bayani

A wani labarin, Garba Shehu, mai magana da yawun tsohon shugaban kasa, Buhari ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa Buhari ya yi gudun hijira.

Shehu ya bayyana haka ne a ranar Lahadi 9 ga watan Yuli yayin mai da martani ga gidajen jaridu.

Ya ce Buhari ya na Daura ne da iyalansa, inda ya shawarci 'yan jaridu su rinka bincike kafin yada labari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel