Gwamnan Kano Ya Mayar Da Daurawa Kan Mukaminsa Na Shugaban Hisbah Ta Kano

Gwamnan Kano Ya Mayar Da Daurawa Kan Mukaminsa Na Shugaban Hisbah Ta Kano

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Gida-Gida ya mayar da Sheikh Aminu Daurawa kan mukaminsa na shugaban Hisbah
  • Shehin malamin ya tabbatar da cewar tuni ya karbi takardar kama aiki a ofishin sakataren gwamnatin jihar
  • Daurawa wanda ya ce ya karbi aikin ne saboda ya ga gwamnati mai ci da gaske take, ya ce zai mayar da hankali wajen aurar da zawarawa

Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-gida ya mayar da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa kan kujerarsa na shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano.

Sashin Hausa na BBC ta rahoto cewa Sheikh Daurawa ne ya tabbatar mata da hakan inda ya ce har ya karbi takardarsa ta kama aiki a ofishin babban sakataren gwamnatin jihar.

Sheikh Aminu Daurawa ya koma kujerarsata na shugaban Hisbah a Kano
Gwamnan Kano Ya Mayar Da Daurawa Kan Mukaminsa Na Shugaban Hisbah Ta Kano Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Asali: Facebook

Daurawa ya ce:

Kara karanta wannan

Dakyar: Bayan shan titsiyen kwanaki a hannun DSS, tsohon gwamnan Arewa ya shaki iskar 'yanci

"Shakka babu a yau na je ofishin sakataren gwamnatin jihar na karbo takardar kama aiki."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sheikh Daurawa da wasu jami'an hukumar Hisbah sun yi murabus daga kujerarsu a watan Mayun shekarar 2019.

Koda dai basu bayar da wani cikakken dalili na yin murabus din nasu ba a lokacin, an yi hasashen cewa sun yi murabus ne sakamakon rashin jituwan da ya gibta tsakaninsa da tsohon gwamna mai ci a lokacin, Abdullahi Ganduje.

A hirar da ya yi da sashin Hausa na BBC, Daurawa ya bayyana cewa ya sake karbar shugabancin Hisbah ne kasancvewar gwamnati mai ci a yanzu ta nuna masa cewar da gaske suke yi za su yi aiki.

Ya ce:

"Sun nuna min cewa da gaske suke yi, sun nuna min cewa da gaske za su yi aiki.

Kara karanta wannan

“Zan Dauki Nauyin Mmesoma Ejikeme”: Miloniya Zai Tura Yarinyar Da Ta Kirkiri Sakamakon JAMB Dinta Waje Karatu

"Dalilina na ajiye aikin a baya shi ne saboda aikin yaki yiwuwa daga karshe-karshe."

Zan mayar da hankali sosai wajen auren Zawarawa, Inji Sheikh Daurawa

Shehin malamin ya kuma bayyana cewa babban abin da zai mayar da hakalinsa a kai shi ne batun auren zawarawa, kamar yadda gwamnan jihar ya yi alkawari.

Ya kara da cewar:

"Gwamnan a yakin neman zabensa ya ce zai aurar da zawarawa da yanmata da kuma taimaka wa harkar iyali da marayu da kuma iyayen marayu, wadanda aka mutu aka bar su da yara. Shi ne abu na farko da za mu sa a gaba."

Ya kuma ce zai dora a kan abubuwa masu kyau da aka yi a Hisbah tare kuma da duba inda za a yi gyara.

Zan ba duk namijin da ya aure ni miliyan 50, gida da mota, Kyakkyawar budurwa

A wani labari na daban, wata kyakkyawar budurwa ta garzaya soshiyal midiya domin neman mijin aure tare da garabasa ga duk wanda ya yi nasarar aurenta.

Matashiyar budurwar ta yi alkawarin baiwa duk wanda ya aureta mota, gida da kuma naira miliyan 50.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel