Karyewar Farashi, Rashin Ciniki Da Sauran Matsalolin Da Suka Addabi Masu Gidajen Mai Bayan Cire Tallafi

Karyewar Farashi, Rashin Ciniki Da Sauran Matsalolin Da Suka Addabi Masu Gidajen Mai Bayan Cire Tallafi

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayu yayin karbar rantsuwar kama mulki
  • Tun bayan cire tallafin mai na shugaban, 'yan Najeriya suka shiga wahalhalu na rashin wadataccen mai kafin daga bisani ya yi tsada
  • Masana tattalin arziki a kasar sun bayyana cewa cire tallafin alkairi ne ga kasar ganin yadda ake biyan kudade da sunan tallafin mai

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Gombe - Tun bayan cire tallafin man fetur a Najeriya da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi, 'yan kasar suka shiga mummunan hali.

Mafi yawan mutane na kokawa kan yadda tsadar mai din ke hana su gudanar da al'amuransu na yau da kullum.

Rashin Ciniki Da Sauran Matsaloli Da Suka Addabi Masu Gidajen Mai Bayan Cire Tallafi
Masu Gidajen Mai Sun Koka Bayan Cire Tallafi. Hoto: Facebook.
Asali: Facebook

Mutanen Najeriya da dama suna cikin wahalhalu musamman yadda kullum kudin sufuri ke kara ta'azzara.

Kara karanta wannan

Hanyoyi 4 Da Za a Bi Don Magance Tsadar Man Fetur a Najeriya, IPMAN

Ana su bangaren masu gidajen mai sun koka bayan cire tallafin inda suka ce ya shafi harkokin kasuwancinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu gidajen mai sun koka kan yadda cire tallafin ya shafe su ta bangarori da dama

Legit.ng Hausa ta zanta da wasu daga cikin manajojin gidajen mai a birnin Gombe da ke cikin jihar Gombe.

Ali Usman wanda shi ne manajan gidan man Ummodah da ke unguwar Dubai a Gombe ya bayyana yadda cire wannan tallafi ya shafe su matuka.

Ya ce:

"Tabbas wannan cire tallafin ya shafe mu sosai, a da kafin cire tallafin a wuni muna iya batar da lita 15,000 zuwa 19,000.
"Amma yanzu ba ma wuce lita 4,000 zuwa 6,000 ka ga kenan an ragu sosai.
"Yanzu ba a siyan mai sosai saboda ya yi tsada kasuwa ta ja baya har ga Allah ba kasuwa."

Kara karanta wannan

'Abokin Kowa': 'Yan Sandan Kano Za Su Buga Wasan Kwallo Na Sada Zumunta Da Tubabbun 'Yan Daba

Da wakilin Legit.ng Hausa ya tambaye shi zargin da mutane ke yi wa masu gidajen mai na boye mai don ya yi tsada, sai ya ce:

"A yanzu duk wanda zai sayi mai ya boye ba shi da tunani, ya za ka sayo mai fiye da 500 ka boye? Idan ya karye fa, saboda yanzu babu kasuwar, a ina zai yi tsada?."

Ya roki Shugaba Tinubu da ya ba da umarnin wadatuwar mai din wanda zai taimaka wurin samar da gasa a tsakanin masu gidajen mai.

Ya ce hakan zai kawo sauki da arahar mayin a kasar baki daya.

Sun musanta jita-jitar cewa IPMAN za ta kara kudin mai

A wata hirar da mataimakin manajan gidan mai na Dan Marna da ke tashar Dukku a cikin garin Gombe, Ibrahim Yahaya Usman ya koka kan rashin ciniki.

Ya ce:

"Gaskiya wannan cire tallafi ba al'umma kadai ba muma ya shafe mu, saboda a baya muna siyar da mota a kwanaki biyu amma yanzu ta na kai mako guda kafin ta kare.

Kara karanta wannan

Har An Fara Murna, Sai AA Rano Ya Musanta Karya Farashin Litar Fetur Daga N540

"Dole a yi hakuri babu yanda aka iya, daman 'yan achaba da sauran masu hada-hadar sufuri ne suka fi shan mai, masu ababen hawa masu zaman kansu wani idan ya sha mai din sai wani wata."

Da wakilin Legit.ng Hausa ya tambaye shi jita-jitar karin kudin mai da Kungiyar Dillalan Mai ta IPMAN ke shirin yi, Ibrahim Yahaya ya karyata wannan zance.

Ya kara da cewa:

"Wannan karyane babu yadda za a yi su kara kudin mai, ai suma sun fito sun karyata, yanzu ya za a yi a rage kudin man ne ba batun kari ba gaskiya.

Ya ce al'umma hakuri za su yi babu yadda za a samar da kudi a kasar idan ta fannin mai ba, inda ya ce idan an yi hakuri duk wannan zai wuce da yardar Allah.

Mai Gidan Man A A Rano Ya Musanta Karya Farashin Litar Fetur Daga N540

A wani labarin, kamfanin A A Rano ya musanta rage farashin man fetur kamar yadda mutane ke yadawa.

Kara karanta wannan

Rahoto Na Musamman: An Bayyana Jihar Da Ka Iya Samar Da Ministan Kudi a Gwamnatin Shugaban Kasa Tinubu

Kamfanin man ya yi maza-maza ya musanta rade-radin inda ya ce babu alamar wannan batu.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa sanarwar ta fito ne daga wani shafi da ake kyautata zaton na kamfanin ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.