Jami'an DSS Sun Kai Samame Harabar Kotu Ana Cikin Shari'a, Sun Kama Mutum 2

Jami'an DSS Sun Kai Samame Harabar Kotu Ana Cikin Shari'a, Sun Kama Mutum 2

  • Jami'an DSS sun kutsa kai cikin kotu ana cikin shari'a, sun tafi da mutum biyu da ake tuhuma a jihar Ogun ranar Talata
  • Lamarin dai wanda ya keta doka ya haifar da hayaniya a harabar kotun, inda lauyan waɗanda ake tuhuma ya caccaki DSS
  • Magatakardan kotun ya bayyana samamen da DSS ta kai a matsayin saɓa wa doka, yana mai cewa sai da alƙali ya hana su kama mutanen

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ogun - Jami’an hukumar tsaro na farin kaya (DSS) sun kai samame wata babbar kotun jiha da ke zamanta a Ilaro a jihar Ogun yau Talata.

Jami'an DSS sun kama biyu daga cikin waɗanda ake tuhuma yayin da ake tsaka da shari'a, lamarin da ya haifar da ruɗani da hayaniya a harabar kotun.

Kara karanta wannan

"Daurarru 400 a Kano ba su san makomarsu a gidan yari ba," Inji 'Yan Sanda

Jami'an DSS.
Jami'an DSS sun kutsa kai cikin harabar kotu a jihar Ogun, sun kama waɗanda ake tuhuma Hoto: @officialDSSNG
Asali: Twitter

DSS ta kama mutane a tsakiyar shari'a

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa waɗanda jami'an suka kama, Alhaji Isiaka Fatai da Samuel Oyero suna fuskantar shari'a ne a ƙara mai lamba HCP/IC/2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun dai na ci gaba da gudanar da harkokin shari'a da ke gabanta karkashin mai shari'a A.A. Shobayo sa'ilin da lamarin ya faru.

Ƙarar dai ta ta’allaka ne kan zargin kone-kone da wani Cif Akeem Adigun, wanda aka fi sani da Socopao, ya shigar da Alhaji Isiaka Fatai, Oyero da wasu mutum 12.

A baya-bayan nan kauyen Agosasa da ke karamar hukumar Ipokia ya faɗa cikin faɗace-faɗace, inda aka yi asarar dukiyoyi na biliyoyin Naira da kuma asarar rai.

Yadda DSS suka kutsa kotun Ogun

Amma an shiga yanayin fargaba yayin da jami'an DSS suka kai samame harabar kotun kuma suka tafi da wadanda ake zargin.

Kara karanta wannan

Dalibai 14 cikin 24 da aka sace a jami'ar Kogi sun kubuta, 'yan sanda sun yi bayani

Lauyan Alhaji Isiaka, Kehinde Bamiwola, a wata sanarwa da ya fitar, ya zargi jami’an DSS da yin amfani da makamai a kan mutanen biyu.

Ya kuma jaddada cewa “An yi wa Alhaji Isiaka Fatai duka, an mare shi, sun ci masa mutinci yayin kama shi."

DSS ta shure umarnin alƙali

Magatakarda kuma shugaban sashin babbar kotun Ilaro, Kwamared Omololu Olusanya, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce sun yi mamaki.

Ya ce duk da alƙali ya umarci jami'an DSS din da kar su kama kowa a harabar kotun amma suka yi fatali da umarnin, suka kama mutanen guda biyu.

"Sun wuce kai tsaye sun yi abin da suka ga dama har suka ci mutuncin ɗaya daga cikin ma'aikatanmu, Misis Fadina. Abin da takaici kuma sun haifar da hayaniya a kotu," in ji shi.

Kotu za ta yanke hukunci kan zaben Kogi

A wani rahoton kuma kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Kogi ta tanadi hukunci kan sahihanci zaɓen Gwamna Ahmed Ododo.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda 4 da jami’an FRSC a wani kazamin hari a Enugu

A zaman kotun na ranar Litinin, 13 ga watan Mayu, kotun ta ce za ta sanar da ranar da za a dawo domin yanke hukunci nan gaba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel