Sallah: Kada Ku Runtumo Bashi Don Siyan Ragon Layya, Gargadin Fitaccen Malami Ga Musulmai

Sallah: Kada Ku Runtumo Bashi Don Siyan Ragon Layya, Gargadin Fitaccen Malami Ga Musulmai

  • Fitaccen malamin addinin Musulunci ya yi gargadi ga al'ummar Musulmi kan runtumo bashi don yin layya
  • Sheikh Muhammad Adewoyin, wanda shi ne babban limamin masallacin Ar-razaq ya ce hakan daurawa kai basussuka ne
  • Ya ce cin bashi don yin layya da dinka sabbin kaya ba dole bane, inda ya ce almubazzaranci haram ne a addini

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kwara - Wani malamin addinin Musulunci, Muhammad Adewoyin ya gargadi Musulmi da su guji cin bashi don ganin son yanka abin layya.

Adewoyin ya bayyana haka ne ga 'yan jaridu a ranar Talata 27 ga watan Yuni inda ya ce yanka a ranar sallah alama ce ta yin biyayya ga ubangiji.

Malamin addini ya gargadi Musulmai kan cin bashi don yin layya
Dabbobi A Kasuwannin Najeriya. Hoto: Legit.ng.
Asali: Facebook

Sheikh Muhammad Adewoyin shi ne babban limamin masallacin Ar-razaq da ke Tanke a Ilorin cikin jihar Kwara, Daily Nigerian ta tattaro.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan da Ake Zargi Ya Sace N70bn Ya Rabawa Mutane Goron Sallar N200m

Ya ce cin bashin rago don layya ba dole ba ne a addini

Ya ce cin bashi don yin layya ba abin burgewa ba ne illa karin wahalhalu da mutane ke kakaba wa kansu, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

"Cin bashi don ganin mutum ya yi layya hanya ce ta kuntata wa kai da kuma karin basussuka akan mutum.
"Sallah ba wata dama ba ce da mutum zai nuna shi mai dukiya ne ko wani kayan alfahari."

Malamin ya gargadi Musulmai kan almubazzaranci a bikin sallah

Malamin addinin wanda kuma mataimakin magatakardan jami'ar Ilorin ne ya ce yin murnar bikin sallah da 'yan uwa da abokan arziki ya halatta a Musulunci, cewar The Nation.

Ya kara da cewa:

"Har ila yau, ana bukatar Musulmai kada su yi almubazzaranci yayin bikin sallar.

Adewoyin ya ce ba dole ba ne sai mutum ya sayi sabbin kayan sakawa da kuma kashe kudade kawai don bikin sallah.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan Ta'adda Sun Kashe Basarake Bisa Kuskure, Sun Sace Mutum 3 a Wata Jihar Arewa

Ya kirayi Musulmai a kasar da suyi bikin sallah cikin natsuwa da taka tsan-tsan.

Bikin Sallah: Sanata Yari Ya Gwangwaje Makwabtansa Da Raguna 500

A wani labarin, Sanata Abdulaziz Yari ya ba da kyautar raguna 500 ga makwabtansa domin yin bikin sallah.

Yari ya yi wannan kyauta ne ga marasa karfi don rage musu radadi a karamar hukumar Talata-Mafara da ke jihar Zamfara.

Shugaban kwamitin rabon ragunan, Alhaji Sha'aya Sarkin Fawa shi ya bayyana haka a ranar Alhamis 22 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel