Sabon Gwamna Zai Ba Mazauna Garuruwa Makamai Domin Yakar ‘Yan Bindiga a Arewa

Sabon Gwamna Zai Ba Mazauna Garuruwa Makamai Domin Yakar ‘Yan Bindiga a Arewa

  • Gwamnan jihar Katsina zai turawa ‘yan majalisar dokoki kudirin kafa Katsina Community Watch
  • Wannan hukuma za ta samu damar daukar mutanen gari aiki da nufin ayi maganin rashin tsaro
  • Idan majalisar jiha ta amince, dakarun da za ayi haya daga kauyuka za su samu horo da makamai

Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya dauki sabon salo da nufin kawo karshen matsalar rashin tsaro da ke addabar mutanensa.

Bayanan da mu ka samu sun ce Mai girma Gwamnan zai tura kudiri zuwa majalisar dokokin jiha da zai taimaka a wajen samun karin jami’an tsaro.

Babban mai taimakawa Gwamnan a dandalin sada zumunta, Isa Miqdad ya shaida cewa kudirin zai bada damar kafa Katsina Community Watch.

Sabon Gwamnan Katsina
Gwamnan Katsina, Dikko Radda Hoto: @Miqdad_Jnr
Asali: Twitter

Idan kudirin ya zama doka, hukumar Katsina Community Watch za ta samu alhakin daukar mazauna garuruwa aikin tsaro a fadin jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa Tinubu Ya Karbi Bakuncin Mai Kudin Afrika, Aliko Dangote a Aso Rock

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda hadimin ya bayyana, za a horas da wadannan mutane, kuma a ba su manyan makamai domin su tunkari ‘yan bindigan da suke yin ta’adi.

Legit.ng Hausa ta fahimci tsohon ‘dan majalisar tarayya, Abubakar Kusada ya yabawa Gwamna Radda a kan wannan mataki da yake shirin dauka.

Ana sa ran hakan zai yi maganin ‘yan bindiga da ake fama da su a wasu garuruwan da ke Katsina.

Bayan ganin sanarwar a shafin Twitter a ranar Asabar, tuni mutane su ka fara yabawa wannan mataki da Gwamna Dikko Umaru Radda ya dauka.

Dokar kasa tayi magana

Wani Lauya a Katsina ya shaidawa mana a tsarin mulki, babu wanda ya isa ya bada izinin rike bindiga, harsashi da alburushi sai gwamnatin tarayya.

Masanin shari’an yake cewa bangaren kundin tsarin mulki ya tabbatar da haka, haka zalika dokar bindigogi ba ta ba Gwamnan jiha damar bada lasisi ba.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida: Sabon Gwamna Ya Sake Fito da Tsarin Zuwa Jami’o’in Kasashen Waje

Abdullahi Machika wanda Lauya ne, ya fadawa Legit.ng Hausa an yi irin haka a Borno, Gwamna Babagana Zulum ya hallatawa ‘yan sa-kai rike bindiga.

An kashe 'dan bindiga'

A daidai wannan lokaci rahoto ya zo daga Katsina Post cewa ‘yan sanda sun kashe wani da ake tunanin ‘dan bindiga ne a karamar hukumar kankara.

Mai magana da yawun bakin rundunar ‘yan sandan reshen Jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya sanar da haka a wani jawabi da ya fitar jiya.

Kamar yadda abubuwa su ke faruwa a jihar Kano, an ji labari haka su ke a Neja inda aka yi sabon Gwamna watau Mai girma Mohammed Umar Bago.

A Katsina, an ji sabon Gwamna Dikko Radda ya karbe duka filayen da Gwamatin baya ta raba ba tare da bin doka ba, kuma za a hukunta masu laifi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel