Bayanai 5 Game da Injiniyan da Zai Zama Gwamnan CBN Bayan Dakatar da Emefiele
- Folashodun Adebisi Shonubi zai canji Godwin Emefiele a matsayin Gwamnan babban banki na CBN
- A karshen 2018, aka nada sabon Gwamnan rikon a matsayin daya daga cikin mataimakan Emefiele
- Da farkon rayuwarsa Shonubi Injiniya ne, said aga baya ya saki layi ya shigar harkar tattalin arziki
Abuja - Folashodun Adebisi Shonubi shi ne wanda zai dare kan kujerar da Godwin Emefiele zai sauka a babban bankin kasa domin a iya yin bincike.
A rahoton nan mun tattaro kadan daga tarihin rayuwa da aikace-aikacen Folashodun Adebisi Shonubi wanda shi zai zama Gwamna na riko a CBN.
1. Haihuwa
Jaridar Vanguard ta ce an haifi Mista Folashodun Adebisi ne a ranar 7 ga watan Maris, 1962, yanzu haka Gwamnan yana da shekaru 61 kenan a Duniya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
2. Karatu da ilmin boko
Daga shekarar 1978 zuwa 1983, Adebisi ya na jami’ar Legas, ya karanci ilmin Injiniyanci. A 1985 ya yi digirgir, ya kware a bangaren hada sinadarai.
Daga shekarar 1988 ne Gwamnan ya saki layi zuwa bangaren tallain arziki har ya samu shaidar digigir a kasuwanci watau MBA, ya kware a fannin kudi.
3. Aikin kamfanoni
Sabon Gwamnan rikon ya fara aiki ne a matsayin Injiniya Mek-ind Associates daga 1984 zuwa 1989, daga nan ya tafi kamfanin Inlaks Computers Limited.
Folashodun Adebisi ya shugabanci sashen asusu na bankin Citibank na shekaru a 1990s, bayan nan ya yi aiki na wasu shekaru uku a kamfanin Agusto & Co.
A kamfanin MBC International Limited ne Adebisi ya zama Mataimakin Manaja wanda ke kula da sashen banki da ilmin zamani na ICT har zuwa 1999.
Daga barin MBC, masanin tattalin arzikin ya karbi kujerar mataimakin shugaba (mai kula da ayyuka da bayanan zamani) a bankin FCMB har zuwa 2002.
Da Ɗumi-ɗumi: Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Sanatan Najeriya Mai Karfin Fada A Ji Ya Rasu A Asibitin Amurka
4. Shiga banki gadan-gadan
Zuwa 2003, jaridar ta ce ma’aikacin ya koma Ecobank Nigeria Plc a matsayin babban Darekta har zuwa 2009 da ya karbi irin wannan matsayi a bankin Union.
5. Gwamnati da mukami a CBN
Kamar yadda aka yi bayaninsa a shafinsa na CBN, tun daga 2012 har zuwa 2018, sabon Gwamnan ne shugaban bankin NIBBS da aka kafa a shekarar 1993.
A Oktoban 2018, gwamnatin Najeriya ta nada shi a matsayin daya daga cikin mataimakan Gwamnonin CBN mai kula da harkar ayyuka a babban bankin.
Emefiele zai bar ofis
A baya rahoto ya zo cewa Mai girma shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin Najeriya, Mista Godwin Emefiele.
Tinubu ya dakatar da Emefiele daga kan kujerarsa a yau Juma’a, 9 ga watan Yuni. Sakataren gwamnatin tarayya ya ce hakan zai bada dama ayi bincike.
Asali: Legit.ng