“Wannan Ya Yi Yawa”: Matashi Ya Rabu Da Budurwarsa Bayan Ya Bankado Sirrinta Da Wasu Maza a Baya

“Wannan Ya Yi Yawa”: Matashi Ya Rabu Da Budurwarsa Bayan Ya Bankado Sirrinta Da Wasu Maza a Baya

  • Wani dan Najeriya ya rabu da wata budurwa bayan ya gano yawan mazan da ta kwanta da su a baya
  • Sai dai kawar matashiyar ya bayyana cewa dalilinsa bai isa da zai rabu da ita ba idan har da gaske yake sonta
  • Jama'a sun yi martani ga lamarin yayin da masu amfani da soshiyal midiya suka caccaki budurwar kan tarayya da maza da yawa haka

Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta hadu da sharrin yin rayuwar rashin tarbiya bayan saurayinta ya rabu da ita sakamakon ganowa da ya yi ta yi mu'amala da maza sosai.

Kawar matashiyar, @nihiinn, ta bayyana a Twitter cewa saurayin ya rabu da ita saboda mutanen da ta kwanta da su sun kai 20.

Hoton wani Mutum da wata matashiya
“Wannan Ya Yi Yawa”: Matashi Ya Rabu Da Budurwarsa Bayan Ya Bankado Sirrinta Da Wasu Maza a Baya Hoto: MoMo Productions, Hill Street Studios
Asali: Getty Images

Ta caccaki hukuncin da mutumin ya yanke, cewa bai isa dalili da zai sa ya rabu da kawar tata ba. Ta rubuta:

Kara karanta wannan

“Ya Ce Kada Na Kashe Duk Abu Mai Rai”: Dan Najeriya Ya Mutu Bayan Dansa Ya Ki Jin Gargadinsa, Ya Kashe Kaguwa a Gidansu

"Wannan gayen ya rabu da kawata saboda jikinta ya hadu da maza kusan 20, gaskiya bana tunanin wannan ya isa dalilin rabuwa da mutum, idan kana sonta da gaskiya."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ta ce mutumin ya ki fada ma kawar tata yawan matan da shi ya hada jiki da su.

"Kuma da ta tambayi mutumin nasa yawan matan da ya hada jiki da su, ya ce lissafi ya kwace masa, toh menene dalilin da zai sa ya rabu da ita."

Kalli wallafarta a kasa:

Jama'a sun yi martani

@jonathan_okoh ya ce:

"Ya danganta da ko yana sonta a ganina yana neman hanyar guduwa ne saboda ba zan yi karya ba muna yin haka sosai idan bama ra'ayin soyayyar kuma ba lallai yana nufin kina soyayya da wani ko ganin wani ba."

@riskandgraceta ce:

"Mutane sun banbanta kamar ke ce da ba za ki yi soyayya da mutumin da ya yi hulda da aminiyarki ba, akwai wasu matan da za su iya."

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaban Kasa Ya Kaddamar Da Ginin Masallacin Majalisar Dokoki Na Miliyan N570

@TheSilvaprta ce:

"20 ya yi kadan ma, na san wata yarinya da ke da 1056 kuma tana zaune lafiya a gidan aurenta da yara uku yanzu."

@NuJhayhne ta ce:

"Na kawata ya kai 50 kuma ta yi aure a watan da ya gabata.
"Maza ba su damu da haka ba."

Budurwa da ta hau jirgin sama da wani bodari ta fadi halin da ta shiga

A wani labarin, wata budurwa wacce ta shiga jirgin sama daga Lagas zuwa Casablanca ta ce akwai wani mutum da ke gurbata iskar da suke shaka.

Matashiyar mai suna @iamrenike a Twitter ta koka cewa fasinjan da take magana a kai yana ta tusa akai-akai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel