Muna Da Litan Mai Biliyan 1.8 Don ’Yan Najeriya, Kyari Ya Fadi Ranar Da Layi Za Kare a Gidajen Mai

Muna Da Litan Mai Biliyan 1.8 Don ’Yan Najeriya, Kyari Ya Fadi Ranar Da Layi Za Kare a Gidajen Mai

  • Mele Kyari, Shugaban Kamfani mai, NNPC ya ce kamfanin ya na da mai lita biliyan 1.8 don da zai wadaci ‘yan Najeriya
  • Kyari ya bayyana haka ne yayin hirarsa da gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis 1 ga watan Yuni a Abuja
  • Mele Kyari ya ba da tabbacin cewa yawan layi a gidajen mai a fadin kasar zai kare zuwa ranar Asabar 3 ga watan Yuni

FCT, Abuja – Shugaban Kamfanin Man Fetur, NNPC, Mele Kyari ya tabbatar da cewa sun adana litan mai biliyan 1.8 wanda zai wadaci ‘yan Najeriya.

Shugaban kamfanin ya kara ba da tabbacin cewa yawan layi da ake samu a gidajen mai ba zai wuce zuwa ranar Asabar 3 ga watan Yuni ba zai kare.

Mele Kyari
Muna da Litar Mai 1.8bn Don ’Yan Najeriya, Kyari Ya Fadi Ranar da Layi Za Kare a Gidajen Mai. Hoto: The Guardian.
Asali: Facebook

Kyari ya bayyana haka ne a yayin hirarsa da gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis 1 ga watan Yuni a Abuja.

Kara karanta wannan

Tinubu Zai Fara Mulki da Ciwon Kai, ‘Yan Kwadago Sun Sa Ranar Shiga Yajin-Aiki

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Ba na tsammanin yawan layin zai wuce kwana daya zuwa biyu, idan ya yi yawa zuwa ranar Asabar, muna da mai a kasa, daman matsalar shi ne rashin wadataccen mai, kuma muna da shi.
“Akwai akalla litan mai miliyan 810 a ajiye a ma’ajiyarmu da tankuna da kuma gidajen mai a fadin kasar, don haka ba a bukatar dauko wa daga kan ruwa zuwa kasa, saboda muna da shi a kasa.”

Ya tabbatar da cewa sanarwar sauya farashin mai din da aka fiskanta a jihohi da dama a ranar Laraba 31 ga watan Mayu a kafar sada zumunta daga kamfaninsu ta fito.

Kyari ya kara cewa tace man fetur din da ake a matatar Dangote da ke Port Harcourt da sauran wurare ba zai sauya farashin mai din ba, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Babban Abokin Faɗan Tinubu Ya Ajiye Kayan Yaƙi, Ya Shirya Zai Karɓi Tayin Kujera

Ya ce matatar Dangote da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar a ranar 22 ga watan Mayu, za ta fara aiki a karshen watan Juli zuwa farkon watan Agusta.

Yayin da ya ce matatar ta Port Harcourt za ta fara a karshen wannan shekara inda ya tabbatar da cewa hakan zai bunkasa samar da man fetur a kasar.

Ya musanta rade-radin da ake cewa farashin man fetur zai yi kasa idan aka fara samar da mai din a gida.

Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ba Ta Da Isassun Kudade Na Biyan Tallafi, Kyari Ya Fadi Dalili

A wani labarin, shugaban kamfanin mai a Najeriya, Mele Kyari ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ba ta da kudin da za ta biya tallafi.

Kyari ya ce duk da cewa kudin tallafin na cikin kasafin kudin shekaru biyu na 2020 da 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel