Cire Tallafin Mai: Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ba Ta Da Isassun Kudade Na Biyan Tallafi, Kyari Ya Fadi Dalili

Cire Tallafin Mai: Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ba Ta Da Isassun Kudade Na Biyan Tallafi, Kyari Ya Fadi Dalili

  • Shugaban Kamfanin Man Fetur, Mele Kyari ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ba ta da kudin biyan tallafin mai
  • Mele Kyari ya bayyana haka ne yayin hira ta gidan talabijin Arise a ranar Alhamis 1 ga watan Mayu a Abuja
  • A shekarar bara, Gwamnatin Tarayya ta ce za ta tsaida biyan kudin tallafin mai daga watan Yuni na wannan shekara

FCT, Abuja – Shugaban Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC), Mele Kyari ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ba ta biya tallafin mai na shekarar 2022 da 2023 ba.

Kyari ya kara da cewa Gwamnatin Tarayya ba ta biya tallafin ba duk da yana cikin kasafin kudi na shekaru biyun.

Mele Kyari
Gwamnatin Tarayya Ba Ta da Isassun Kudade Na Biyan Tallafin Mai. Hoto: The Guardian.
Asali: Facebook

Mele Kyari ya bayyana haka ne yayin da yake amsa tambayoyi a hirarsa da gidan talabijin na Arise a ranar Alhamis 1 ga watan Yuni, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Shekarau Ya Yo Hangen Nesa Ya Ba Tinubu Muhimmiyar Shawara Kan Cire Tallafin Man Fetur

Kyari ya na magana ne akan cire tallafin mai da Shugaba Tinubu ya yi bayan tashin farashin litar mai a fadin kasar wanda ya kawo wahalhalu ga mutane.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnatin Tarayya ta ce za a tsaida biyan kudin a watan Yuni

Daily Post ta tattaro cewa a shekarar bara, Gwamnatin Tarayya ta ce za a tsaida biyan kudin tallafin mai din daga watan Yuni na wannan shekara.

Gwamnati ba ta samar da kudaden biyan tallafin ba, Kyari

Amma a cewarsa, banda rashin iya biya kudin tallafin da kamfanin ya yi, Gwamnatin Tarayya har yanzu ba ta samar da kudade na biyan tallafin ba tun farkon wannan shekara.

A cewarsa:

“Matsalar anan ita ce, kasar ba ta da kudin da za ta ci gaba da biyan tallafin.
“An samar da tiriliyan 6.3 a shekarar 2022 da kuma tirilian 3.7 na shekarar 2023 har zuwa tsakiyan shekara, amma ko kwabo ba a biya ba kuma dole zamu biya haraji da sauran abubuwan da suka zama dole saboda babu yadda zamu yi.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani a Ganawar Tinubu da Kungiyar Kwadago

“Dole a biya tallafi saboda doka ta ce gwamnati za ta rubuta cak a karshen ko wane wata ga NNPC saboda biyan kudin aikin da suka wa kasa, ba a rubuto cak din ba ko sau daya."

NNPC Ya Tura Sako Ga ’Yan Najeriya Bayan Tinubu Ya Cire Tallafin Man Fetur

A wani labarin, Kamfani mai na NNPC ya bayyana goyon bayansa akan cire tallafin da Shugaba Tinubu ya yi.

Bola Tinubu ya fadi haka ne yayin bikin rantsar da shi, inda ya ce daman ba a saka gurbin biyan tallafin ba a kasafin kudi na 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel